✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma sun yi asarar shinkafa kashi 80 sakamakon ambaliya a Kebbi

An samu akasin yadda ake samun amfanin noman shinkafa a garuruwan Jihar Kebbi bayan girbe shinkafar da aka shuka lokacin damina. Noman shinkafa na yankunan…

An samu akasin yadda ake samun amfanin noman shinkafa a garuruwan Jihar Kebbi bayan girbe shinkafar da aka shuka lokacin damina.

Noman shinkafa na yankunan Fadama ya samu matsala saboda kwanciyar ruwa a gonakin shinkafar.

Yankunan Fadama biyu da aka fi shuka shinkafar su ne: yankin kogin Rima da kogin Neja wurare ne da ke albarkar noman shinkafa saboda yawan shinkafar da ake girbewa a yankunan.

Sai dai wannan daminar ta bana ambaliyar ruwan ta mamaye wasu yankunan jihar, inda hakan ya zama wani koma baya ga manoman jihar. Mafi yawancin manoman Fadama da ke yankunan kogin Rima da kogin Neja amnbaliyar ruwa ta lakume kashi 80 cikin 100 na shinkafar da manoman suka shuka.

Shugaban kungiyar manoma shinkafa (RFA) a jihar Kebbi Alhaji Muhammed Sahabi Augie, ya ce, an yi asarar shinkafar da aka noma ne sanadiyyar ambaliyar ruwa.

Alhaji Muhammed ya ce, noman shinkafa ya samu tangarba a yankunan da ake noman Fadama, manoman yankin kogin Rima sun yi babbar asarar shinkafa da ya kai kashi 80 cikin 100 da kuma kogin Neja da ya kai kashi 30 cikin 100 duk sanadiyyar ambaliyar ruwa. A yankunan garuruwan Zuru da Yauri inda ake girban shinkafa mai bimbin yawa, akwai bukatar bunkasa noman shinkafa a babi don maye gurbin asarar da aka yi.

Abin alfaharin shi ne manoman jihar Kebbi na noman shinkafa a kowa ne yanayi a shekara, akalla wata biyar zuwa shida na kowace shekara kafin a sake girbe abin da aka shuka. Akwai bukatar gwamnati ta sake bube wasu wurare don noman shinkafa wanda hakan zai sa a samu amfani mai yawa a jihar.

Augie, ya ce bayan tallafin rancen kubin da gwamnati da take baiwa manoma na ‘Anchor Borrowers Programme (ABP)’, ya kamata gwamnati ta kaddamar da abubuwan da zai bunkasa nomann shinkafa a jihar.

Wani manoma a shiyyar gonakin Makera da ke karamar hukumar Birnin Kebbi ya bayyana wa wakilinmu cewa, da kyar ya samu ya girbe kashi 20 cikin 100 na shinkafar da ya shuka, makonni kaban kafin ya girbe ambaliyar ta auku a gonar. “Na yi sa’a da na samu kaban daga cikin abin da na shuka yayin da wasu manoman basu sami komai ba a gonakinsu sanadiyyar ambaliyar ruwa”, inji manomin.