✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoma sun yi zanga-zanga  kan zargin Dangote da kwace gonakinsu a Nasarawa

A karshen makon jiya ne wadansu manoma da suka fito daga Karamar Hukumar Awe a Jihar Nasarawa suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin…

A karshen makon jiya ne wadansu manoma da suka fito daga Karamar Hukumar Awe a Jihar Nasarawa suka gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin amincewarsu da yunkurin kwace musu gonaki da suka kai fadin hekta dubu 18 da ake zargin Kamfanin Dangote na kokarin yi.

Manoman wadanda suke rike da kwalaye masu rubutu daban-daban na bayyana rashin amincewa da yunkurin ta bakin jagoransu Alhaji Ibrahim Rilwanu sun ce, a kwanakin baya Kamfanin Dangote da hadin gwiwar gwamnatin jihar sun kwace musu filayen gonakinsu da suka kai sama da hekta dubu 80 da nufin gina kamfanonin sukari da na noman shinkafa da sauransu amma har yanzu ba a biya galibinsu diyyar filayen ba.

Jagoran masu zanga-zangar ya ce, garuruwa da kauyukan da kamfanin ke yunkurin mallakar filayen manoman sun hada da Dankan-Duniya da Dankan-Buhari da Kwante da Kekura da Kafin-Moyi da Barkonu da Pantaki da Kwakwanondo da Bakin-Kogi duk a Karamar Hukumar Awe. Ya bayyana takaicinsa dangane da lamarin inda ya ce, wannan yunkurin zai sanya kimanin manoma dubu 50 da ke yankin su rasa gonakinsu inda ya ce gonakinsu ba na sayarwa ba ne.

Ya ce, “Gwamnatin jihar nan ta korar mu daga aiki tun a shekarar 2011 kuma har yanzu ba ta ba mu aiki ba. Shi ya sa muka dukufa ga aikin noma. Saboda haka ba za mu yarda Kamfanin Dangote ko wani kamfani daban ya kwace mana  gonakinmu ba, domin su ne hanyoyin neman abincinmu a yanzu. Shi ya sa muke zanga-zanga don nuna rashin amincewarmu a kan karba ko kwace mana gonakinmu ba bisa ka’ida ba da kamfani da gwamnatin jihar ke yunkurin yi a yanzu.”

Ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta gaggauta sa baki a lamarin don kauce wa tashin hankali da hakan ka iya jawowa a yankin da jihar, inda ya ce, a yanzu haka rayukan manoman yankin na cikin hadari, saboda a cewarsa kamfanin ya hada gwiwa da mahukuntan karamar hukumar inda suke turo musu jami’an tsaro suna tilasta su barin gonakinsu suna ci musu mutunci.

Sai dai da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Karamar Hukumar Awe, Alhaji Umar Tanko Ban-Kano kan lamarin, ya ce, karamar hukumar da hadin gwiwar gwamnatin jihar ne suka ga ya dace ne su samar wa Kamfanin Dangote isasshen fili bayan sun fahimci ayyukan ci gaba da kamfanin zai kawo wa jihar musamman a yankin ta hanyar kaddamar kamfanonin sarrafa sukari da noman shinkafa na zamani da sauransu, don bunkasa tattalin arzikin jihar.  Ya ce galibin manoman yankin sun ki amincewa da haka.

“Da kaina na zanta da manoman daga yankunan dangane da muhimmancin yunkurin amma suka ki amincewa. Bayan haka ban ce komai ba ban tilasta wa kowa ba. Haka kuma ban umarci wani jami’in tsaro ya tilasta wa kowa ba. Sai kawai daga baya na ji wai suna zanga-zanga a kan lamarin. Abin ya ba ni mamaki matuka.,” inji shi.

Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Kakakin Kamfanin Dangote da ke yankin, Alhaji Sa’idu Mohammed dangane da lamarin inda ya ce, kamfanin yana bin duk ka’idojin da suka dace musamman na biyan manoman hakkinsu kafin ya karbi filayen daga wajensu. Ya ce, wadansu ’yan adawa ne da ba sa son ci gaban jihar nan ke yin amfani da wadansu manoma a jihar don cimma burinsu na dakile kokarin da kamfanin ke yi na kawo gagarumin ci gaba da zai canja rayuwar al’ummar jihar.

“Kamar yadda kuka sani wadansu ’yan siyasa ’yan adawa ne da suka saba mayar da komai siyasa ke amfani da wadansu manoma a jihar nan don maido da hannun agogo baya, a kokarin da gwamnatin jihar da hadin gwiwar Kamfanin Dangote ke yi na kawo canji mai ma’ana a rayuwarsu baki daya. Amma ina tabbatar muku cewa ba za su yi nasara ba,” inji shi.

Ya bukaci al’ummar jihar su yi watsi da zargin don ba ya da tushe.