✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman auduga za su samar da tan dubu 300 a badi

Manoman auduga a karkashin kungiyarsu ta kasa, sun ce a badi suna sa ran samar da tan din auduga sama da dubu 300. Hakan na…

Manoman auduga a karkashin kungiyarsu ta kasa, sun ce a badi suna sa ran samar da tan din auduga sama da dubu 300.

Hakan na zuwa ne sakamakon karin kudin tallafin noma da manoman suka samu daga Babban Bankin Najeriya (CBN) a karkashin shirin bankin na bunkasa noman auduga.

Babban Manajan Darakta kuma Shugaban Gudanarwa na Kungiyar Manoman Audugar a Shiyyar Arewa  kuma Shugaban Kungiyar ta Kasa, Mista Anibe Achimugu, ya bayyana haka a lokacin wani taron masu ruwa- da-tsaki da kuma shugabanni da sakatarorin jihohin, inda suka tattauna yadda za su tattara audugar da kuma mayar da rancen da aka ba su a Abuja.

Mista Achimugu, wanda aka sake zabarsa ba tare da hamayya ba a karo na biyu a matsayin shugaban kungiyar ya ce tun zamansa shugaba, ya tabbatar da suna da sahihan manoma masu rajista kimanin dubu 151; kuma sun samu damar  shiga a dama da su a shirin bada rancen noma na ‘Anchor Borrowers’ inda kowannensu ya samu irin shuka da kudi da suka kai na Naira dubu 170.

Babban jami’in ya ce kungiyar tana aiki da Babban Bankin Najeriya don kara farfado da noman auduga a badi, sannan suna sa ran samar da karin tan-tan din auduga da suke nomawa zuwa tan dubu 300, wanda koda mutum daya zai noma kadada daya ne za su iya samar da haka.

“Da nake magana da ku a yanzu haka muna da wajen kadada dubu 200, amma muna sa ran samun yabanya ta tan 1.5 zuwa tan 2 a kowace  kadada.

Sai dai a bara muna samun matsakaicin kilo 500 zuwa 600 a kowacce kadada, amma yanzu muna da iri mai kyau da idan muka mayar da hankali za ku ga abin da za mu samu,” inji shi..

A cewarsa, shugaban manoma sun samu tabbacin Bankin CBN na bunkasa noman auduga a kasar nan.