Da Dumi Dumi

Manoman dawa dubu 36 za su samu tallafin Naira biliyan 6 a Gombe

Shugaban Qungiyar Manoman Dawa ta Qasa a dama yake miqa wa wani Basarake manomi maganin feshi da irin dawa

A ranar Litinin da ta gabata ce Kungiyar Manoman da Masu Kasuwancin Dawa ta Kasa, (National Association of Sorghum Producers, Processors and Marketers of  Nigeria – NASPPAM) ta kaddamar da bai wa manoman dawar  iri da maganin feshi da sauran kayan gona don bunkasa noman dawa a Jihar Gombe.

Bikin ya gudana ne a garin Bajoga helkwatar Karamar Hukumar Funakaye da ke jihar, kuma Shugaban Kungiyar  NASPPAM ta Kasa Alhaji Babayo Maina, ya ce kungiyar za ta raba kayayyakin ne bashi ga manoma sama da dubu 36 a fadin jihar.

Ya ce su ne a kungiyance za su kawo ’yan kasuwa kusa don sayen amfanin da manoman suka noma a farashi mai kyau.

Alhaji Babayo Maina, ya jawo hankalin manoman cewa idan aka ba su wannan kaya za su biya ne da amfanin gonar da suka noma a zangon noma uku inda a farko za su ba da kashi 40; kana a zagaye na biyu da na uku za su ba da kashi talatin-talatin.

Ya ba su shawarar cewa su daure su mayar da bashin don wadansusu samu. “Ku yi koyi da wadanda NECAS ta bai wa rance suka mayar wanda hakan  ya sa yanzu shirin na NECAS ya ci gaba bai tsaya ba,” inji Maina.

ADVERTISEMENT

Sai ya yaba wa Gwamnan Jihar  Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya kan yadda yake bai wa harkar noma kulawa a jihar inda daga hawansa mulki ya kaddamar da sayar da taki ga manoma a farashi mai sauki.

A tsokacin Babban Sakataren Ma’aikatar Aikin Gona ta Jihar, Barista Obel Yaji, wanda Usman Wawa, ya wakilta ya jan hankalin manoman ne cewa su mayar da hankali wajen noma dawar yadda ta dace domin iri ne mai jure fari da kuma nuna da wuri.

Barista Yaji, ya ce saboda kulawar da Gwamna Inuwa ke yi wa manoma a jihar ya sa a makon jiya aka yi feshin tsuntsaye jan-baki da suka addabi wasu kananan hukumomin jihar biyar.

Shugaban Kungiyar Manoman Dawa a jihar Alhaji Sale Shu’aibu, ya ce wannan taro na bai wa manomansu tallafi shi ne irin sa na farko da kungiyar ta fara yi a ko’ina a kasar nan.

Ya ce kungiyarsu ta kunshi komai domin idan manomi ya yi noma su za su kawo ’yan kasuwa da za su sayi amfanin a farashin da ya kamata don amfanin manomi.

Shugaban Kungiyar NECAS a Jihar Gombe Alhaji Ahmed Muhammad Dukku, ya jawo hankalin manoman cewa kada a ba su kaya a matsayin bashi su sayar su yi bushasha. Ya ce su sani bashi ne kuma za su biya.

Alhaji Ahmed  Dukku, ya ce yana fata za su yi koyi da manoman da NECAS ta bai wa kaya suka dawo da shi ba tare da wata matsala ba.

Share