Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Manoman Jihar Kebbi sun yi sharar gona don shuka gero a bana

Wata gonar gero

Manoman gero a Jihar Kebbi sun fara sharar gonakinsu da nufin noman gero da zarar daminar bana ta sauka.

Manoman dai yanzu suna jiran faduwar ruwan sama a daminar bana ce don shuka geron kamar yadda wani manomi da ke da gona a hanyar titin zagaye da ke Birnin Kebbi ya bayyana wa wakilinmu. Ya ce yana yin aikin gyaran gonarsa ce domin shirin yin shukar gero da zarar ruwan sama na ya sauka a jihar. Ya ce, ‘‘Lokacin shukar gero yana karatowa, don haka ina kokarin yin duk aikin da ya kamata in yi kafin saukar ruwan sama.’’

ADVERTISEMENT

Kuma ya ce, ‘‘Manoma a Jihar Kebbi suna hasashen samun ruwan sama a cikin watan Afrilun nan da muke ciki.’’

Kazalika wadansu manoman sun bayyana cewa ‘‘Mun soma shukar gero a bara a cikin watan Mayu saboda mun yi shuka a makare. Saboda haka muna hasashen cewa damunar bana za ta soma sauka da wuri.”

ADVERTISEMENT

Shi ma wani manomi daga Karamar Hukumar Kalgo, Ibrahim Garba Bunza, ya ce, ‘‘Na soma gyaran gonata mai fadin hekta uku don in shuka gero.” Kuma ya kara da cewa ya sayi irin gero da taki da sauran abubuwan aiki don yin shuka da zarar ruwan sama ya sauka.

Ya ce, ‘‘Na amfana da tallafin da gwamnatin Jihar Kebbi ta bayar ga manoman gero a bara.’’

Ya ce, ‘‘An ba mu iri da taki da kuma magungunnan kwari, saboda haka muna sa ran cewa a bana gwamnatin jiha za ta taimaka wurin ganin ta ba da wannan tallafin ga manoman damina.

Su ma manoman garuruwan Buku da Makera da na sauran wurare a Karamar Hukumar Birnin Kebbi sun soma yin ramun shuka wadanda jiran saukar ruwan sama kawai suke yi. Wani manomi mai suna Mustapha Sulaiman ya ce ya soma aikin gyaran gonakinsa da ke a garuruwan Ambursa da Zauro da Gwadangaji da ke Birnin Kebbi.

Malam Mustapha ya kara da cewa, ‘‘Akwai bukatar in fara aikin gyaran gonakina a kan lokaci saboda irin darasin da na samu a bara. Saboda bara na fara a makare wanda haka ya sa na gamu da matsaloli da ba na tunaninsu.Yanzu kuwa duk abin da ya kamata in tanada don yin aikin bana na tanade shi don kauce wa abin da ya faru a bara.”

Haka kuma ya ce, ‘‘Na sayi takin zamani da sauran kayan da ake aikin noma da su. Yanzu abin da nake jira kawai saukar ruwan sama don shuka gero.