✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman rani a Jihar Sakkwato sun samu kananan motoci noma 60

Hukumar Kula da Kogin Rima, ta ce ta fitar da kananan motocin noma 60 da za ta rika bai wa manoman rani haya a jihohi…

Hukumar Kula da Kogin Rima, ta ce ta fitar da kananan motocin noma 60 da za ta rika bai wa manoman rani haya a jihohi hudu na yankin a karkashin shirin noman rani na hukumar.

Farfesa Ahmad Ala, Daraktan Noma, na Hukumar ne ya sanar da manema labarai haka a birnin Sakkwato.

Dokta Ala ya ce shirin ba da hayar motocin noman, hukumar ta fito da shi ne domin kara bunkasa noman rani a jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kebbi.

Ya ce ana daukar wadannan matakai ne domin kara karfafa hanyoyin noman zamani da kara shigo da manoma cikin kasuwanci abin da zai kara yawan amfanin gona.

Daraktan na SARBDA, ya ce suna kula da noman rani a kananan hukumomi takwas da suka hada da Goronyo da Bakalori da Zauro da Shagari da Jibiya da wasu hudu da hukumar Rima ke kula da su a jihohin.

Ya ce kowace mota an hada ta da jami’in da zai rika kula da yadda ake aiki da ita, don sanin aikin da ta yi da inda take aikin da kudin da aka karba da sauran wasu bayanai da suka shafi  amfani da ita.

Dokta Ala ya ce wadannan bayanai suna taimakon shirin bayar da motocin noma akan ajiye su ga duk wanda yake bukatar bayanan.

Ya ce sababbin dubarun noma suna kan hanya, inda ya ce duk wata hanya ta inganta noman rani na zamani suna maraba da ita.

Ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan kokarinta na karfafa Kogin Rima; inda ya ce kuma ba abin da hukumarsu ke yi, sai kula da wannan  kogi a jihohin hudu.

Dokta Ala ya ce hukumarsu na huldar kasuwanci da kamfanonin WACOT da Dangote don samar da inganci ga kayayyakin da shirin ke samarwa.

Daraktan ya ce za su ci gaba da hada kai da kamfanonin sayen amfanin gona da masu kula da shirye-shiryen noman rani don samun nasarar shirin.