✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman shinkafa dubu 90 suka amfana da bashin noma – RIFAN

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kano, ta ce kimanin manoman shinkafa dubu 90 ne suka amfana daga bashin noma na Babban Bankin…

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen Jihar Kano, ta ce kimanin manoman shinkafa dubu 90 ne suka amfana daga bashin noma na Babban Bankin Najeriya (CBN) a cikin shekara uku, wato daga shekarar 2017 zuwa 2019 .

Shugaban Kungiyar, Alhaji Haruna Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka, inda ya musanta zargin cewa Jihar Kano ba ta amfana daga shirin tallafin noma na Gwamnatin Tarayya ba.

Ya ce, manoman shinkafa da suka hada da na rani da na damina duk sun samu bashin noman a jihar.

“Babu kanshin gaskiya mutum ya fito ya ce wai manoman Jihar Kano ba su samu bashin noma daga Gwamnatin Tarayya ba. A shekarar  2017 kimanin manoma dubu 24 ne daga rukuni takwas suka amfana. Haka a shekarar bara manoma dubu 44 daga rukuni 11 ne suka samu wannan tallafi na noman damina. Kuma a bana, manoma dubu 28 daga rukuni bakwai suka amfana daga tallafin,’’ inji shi.

Shugaban ya ce batun a ce mutum yana da kadada dubu 200 yana kuma girbar shinkafa  buhu 250 daga kowace kadada ba tare da tallafin gwamnati ba wannan ba abu ne mai yiwuwa ba.

Abu ne da ya fi kama da kambame, “Kungiyarmu ta girgiza da jin cewa wani mutum ya fadi cewa wai manoman shinkafa na Jihar Kano ba su amfana daga bashin na Gwamnatin Tarayya ba,”  inji shi.