✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman shinkafa na sa ran darawa a bana a Kano da Yobe

Mamoman shinkafa a Jihar Kano, na fatar samun amfanin shinkafa mai yawan gaske, lura da sababbin dabarun noma da Kungiyar Sassakawa Afirka tare da hadin…

Mamoman shinkafa a Jihar Kano, na fatar samun amfanin shinkafa mai yawan gaske, lura da sababbin dabarun noma da Kungiyar Sassakawa Afirka tare da hadin gwiwa da Hukumar Aikin Gona da Raya Karkara ta Jihar suka kirkiro da su, don bunkasa samar da shinkafar.

Da yake jawabi ga Kungiyar Sassakawa da sauran masu ruwa-da-tsaki a fagen habaka noma, jagoran kungiyar manoman shinkafa na Bugau a Karamar Hukumar Kura a Jihar Kano, ya ce lura da wadannan sababbin dabarun noman da samar, suna da kwarin gwiwar shinkafar da za su girba ta dara yadda suka saba a baya.

“Mun fara ganin bambamci tun gabanin girbin. Sababbin dabarun ba su ma ci mana mana kudi irin yadda muka saba ba; kuma bisa dukkan alamu idan ka yi dubi a tsanake ga gonakin shinkafar, lallai za ka fahimci manoman za su dara; kuma za a girbi amfani mai yawan gaske,” inji shi.

“Mun dabbaka sababbin dabarun shuka da zuba taki tare da amfani da sabon irin shuka. Wadannan bakin ababuwa ne gare mu; sai dai mun rungume su, kuma ba mu yi nadamar haka ba,” injii Shugaban Manoman Bugau.

Da yake jawabi ga manoman, Daraktan Sassakawa a Najeriya, Farfesa Sani Miko, ya fada wa manoman cewa, ayarinsu zai yi rangadi don nazartar tasirin sababbin dabarun.

A wani labarin kuma a Jihar Yobe bayanai sun nuna manoma za su dara a bana a jihar.

Manoma a Damaturu sun nuna jin dadinsu dangane da yanayin damina tare da hasken ranar da ake samu wadanda za su taimaka wajen inganta amfanin gona a bana. Manoman da suka zanta da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), sun ce daminar sai dai tubarkalla, lura da yadda ake samun karamar tazara a tsakanin ruwan sama, wanda hakan ke faranta zukatan manoman.

Alhaji Makinta Bukar, wani tsohon ma’aikacin gwamnati da ya rikide ya zama manomi, ya ce: “Ba kamar a bara ba, inda ruwan sama ya yi ta kafewa a  kai-kai; a bana tubarkalla.

Malam Musa Mohammed, karamin manomi ne, ya ce: “Da farko cikin manoma ya duri ruwa, bisa tsaikon saukar damina; amma daga baya ta daidaita, kuma amfanin ya inganta.”

“Kusan duk yankin jihar nan; ya samu ruwan sama ba tare da fuskantantar wata barna ba; zuwa yanzu dai ba a samu rahoton ambaliya ba,”  inji shi.

Wani manomi, Malam Usman Ali, ya ce sabon amfanin kusan ya gama nuna: “Wadanda suka yi shukar farko, na sa ran girbe amfanin cikin makonnin da ke tafe,” inji shi.

Wani manomin mai suna, Malam Maina Suleiman, ya fada wa Kamfanin NAN cewa zuba taki a kan lokaci ya taimaka gaya, wajen kyautata samun yabanya mai kyau.

Har wa yai a wani labarin, Gwamnatin Jihar Yobe, ta sanya  hannu kan wani kwantiragi don samar da takin zamani mai nauyin tan 9000, nau’in NPK da kuma taraktocin noma kirar Massey Ferguson, guda 40, domin noma a daminar 2019.

Da yake rattaba hannu kan kwantiragin, a madadin gwamnatin jihar, Babban Sakataren Ma’aikatar Gona ta Jihar, Alhaji Mangarima Lawan, ya ce an saka hannu a kwantiragin takin ne a kan Naira biliyan 1 da miliyan 701; yayin da kwantiragin taraktocin noman kuma zai ci Naira miliyan 882.

Babban Sakataren, ya yi kira ga ’yan kwangilar da su yi maza wajen samar da kayayyakin, bisa tsarin da aka cimmawa.

“Gwamnati a shirye take ta zuba kudi kashi 30 cikin 100 cikin asusunku; a matsayin kafin alkalami, da zarar mun samu lamuni daga kamfanoninku,” inji Babban Sakataren.

“Wadannan abubuwa guda biyu, su ne manyan kalubalen da ke ci wa manoman jihar nan tuwo a kwarya; hakan ne ya sa gwamnati ta ga dacewar samun kwararru sun samu kwantiragin kawo kayayyakin ga manoman, don haka kada ku kuskura ku yi kwange a ciki,” Babban Sakataren ya yi gargadi.

Wakilan kamfanonin Ponglomerape Nigeria Limited da Mantalli Nigeria Limited, wadanda suka saka hannu a kwantiragin, sun yi godiya ga gwamnatin jihar, bisa abin da suka kira ‘amincewarta da ta yi da su, wajen ba su kwantiragin’ tare da tabbatar da samar da kayayyakin a kan lokaci.