✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman tumatur a Sakkwato sun samu ingantattun iri

Hukumar Bincike da Kula da Ci gaban Albarkatun Kasa ta gabatar da sababbin ingantattun irin tumatir ga manoman kayan miya a Jihar Sakkwato. Hukumar ta…

Hukumar Bincike da Kula da Ci gaban Albarkatun Kasa ta gabatar da sababbin ingantattun irin tumatir ga manoman kayan miya a Jihar Sakkwato. Hukumar ta yi wannan gwaji ne a jihohi takwas da suka hada da Filato da Kano da Kaduna da Neja da Gombe da Taraba da Oyo da Benuwai. Shugaban Majalisar Zartarwar Hukumar, Alhaji Abdullahi Waziri Tambuwal, ya ce wannan yunkurin an fito da shi ne da zimmar magance gibin bukata da amfani da ake da shi ga masana’antun kasar nan.

Ya ce suna kokarin samar da amfanin gona masu inganci a Najeriya. “Noman tumatir a kasar nan yana dagawa a halin yanzu ana samar da tan miliyan 1.8 na tumatir, a kasa baki daya ana bukatar tan miliyan 2.4 a shekara, akwai gibi sosai,” inji shi.

Ya yaba wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, kan goyon baya da kawo ci gaba a fannin noman tumatir a jihar da kasa baki daya.

Kwamishinan Aikin Gona na Jihar Sakkwato, Alhaji Arzika Tureta, ya yaba wa basirar da tabbatar da karin goyon baya tare da hada kai don nasarar shirin noman tumatir din.