Aminiya

Manomi da ’ya’yansa uku

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe. Tare da fatar kuna cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin “Manomi da ’ya’yansa uku.” Labarin ya yi nuni ne ga yadda kokari da hazaka ke kawo ci gaba a rayuwar dan Adam. A sha karatu lafiya.

An yi wani manomi wanda yake da ’ya’ya maza uku. Manomin bai da wata hanyar samun kudi da ta wuce noma. ’Ya’yan nasa kuma babu abin da suka fi iyawa illa a yi musu abinci su ci su kwanta.

Kullum manomin yana kiransu su rika taimaka masa a gona amma hakan ya gagara sakamakon yawan son jiki irin na ’ya’yansa.

A kwana a tashi har tsufa ta tarar da manomi sannan jinya ta kama shi. Yana tsoron yadda rayuwar wadannan ’ya’yan nasa maza ukun za ta kasance bayan ya rasu.

Za mu ci gaba

ADVERTISEMENT