✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mansur Lawal: dan jarida mai kwazo ya kwanta dama

Alhaji Mansur Lawal Isma’il, kwararren dan jarida ne wanda ya share kimanin shekara 27 yana aiki da kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta…

Alhaji Mansur Lawal Isma’il, kwararren dan jarida ne wanda ya share kimanin shekara 27 yana aiki da kamfanin buga jaridun New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo, kuma kafin rasuwarsa a ranar Juma’a 26 ga Satumban 2014, shi ne Babban Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo.
Alhaji Mansur Lawal, ya fara aikin jarida ne bayan ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda a farkon fara aikinsa aka tura shi garin Bauchi a farko shekarun 1987 a matsayin wakilin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo daga baya ya zama wakilin jaridar Ingilishi ta kamfanin wato New Nigerian, a yayin zamansa a Bauchi ne ya zama shugaban kungiyar Wakilan Kafafen Watsa Labarai (Correspondent’s Chapel), na Jihar Bauchi.
Bayan ya share shekaru a Jihar Bauchi sai aka yi masa canjin wajen aiki aka mayar da shi garin Damaturu na Jihar Yobe, kuma yana wannan aiki har aka kirkiro da Jihar Gombe a 1996 inda a 1997 aka dawo da shi jihar ya jagoranci bude ofishin jaridar New Nigerian a jihar. Yayin zamansa a jihar ya zama shugaban kungiyar Wakilan Kafafen Watsa Labarai (Correspondent’s Chapel), na jihar na farko kuma wanda ya fi kowane shugaba jimawa a kan wannan matsayi.
Alhaji Mansur Lawal ya ci gaba da aiki a jihar har dawowar mulkin farar hula inda ya yi zamani da tsohon Gwamnan Jihar Gpmbe na farko na farar hula a tsohuwar Jam’iyyar APP Alhaji Abubakar Habu Hashidu a tsakanin 1999 zuwa shekarar 2003. Bayan shudewar gwamnatinsa a shekara ta 2003 lokacin da Alhaji Muhammad danjuma Goje, ya zama Gwamna  a Jam’iyyar PDP, ya nada Alhaji Mansur Lawal a mukamin mai taimaka masa a bangaren aikin jarida (S.A Media) a shekara ta 2010, wato lokacin zangon Gwamnan karo na biyu.
Alhaji Mansur Lawal, ya samu mukamin Sakataren Watsa Labarai na Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ne a shekara ta 2011 har zuwa lokacin da Allah Ya karbi ransa a ranar Juma’ar makon jiya wato 26 ga Satumban bana.
Babban Sakataren Ma’aikatar Watsa Labarai na Jihar Gombe Mista Kelmi John Lazarus, ya bayyana Mansur Lawal a matsayin kwararre, haziki, mai hakuri kuma masanin aikin jarida wanda ya ba da gudumawa mai gwabi wajen ganin aikin jarida ya ci gaba.
Mista Kelmi Lazarus, ya ce Mansur Lawal, mutum ne wanda bai fushi da mutane a sha’anin aiki sannan mutum ne mai haba-haba da jama’a wanda a kullum burinsa shi ne ganin duk wani dan jarida a jihar da na waje ba su sami matsala ba a lokacin da suka zo Gombe don gudanar da aikinsu.
Wasu ’yan jarida da wakilinmu ya zanta da su kan rasuwar marigayin sun nuna jimaminsu da alhinin rasuwar Mansur.
Shugaban kungiyar ’Yan jarida ta Jihar Gombe Alhassan Muhammad Yaya, jajanta wa ’yan jaridan jihar ya yi bisa rashin Mansur Lawal, inda ya ce mutum ne haziki mai kaunar abokan aikinsa a kullum.
Alhassan Yaya, ya kuma bayyana rasuwar Mansur a matsayin babban rashi ba ga ’yan jarida da iyalansa kadai ba, rashi ne ga Jihar Gombe da kasa baki daya, ya ce duk da cewa Mansur dan asalin garin Zariya ne a Jihar Kaduna amma ko can ba a more shi kamar yadda Jihar Gombe ta more shi.
Shugaban ya kuma yi wa iyalan marigayin ta’aziyya da addu’ar Allah Ya ba su hakurin jure wannan babban rashi.
Ita ma kungiyar wakilan kafafen watsa labarai ta jihar ta bi sahun wakilan gwamnatin jihar zuwa garin Zariya don yi wa iyalan mamacin ta’aziyya inda shugaban kungiyar Mista Timothy Choji na Muryar Najeriya ya jagoranta.
Marigayi Mansur Lawal, ya samu kyakkawan shaida a tsakanin abokan sana’arsa ’yan jarida da al’ummar Jihar Gombe bisa yadda yake tafiyar da mutane wajen rungumar kowa ba tare da nuna kyama ko bambancin akida ko jinsi ba.
Marigayin ya rasu yana da shekara 54 ya kuma rasu ya bar matan aure biyu Halima Yusuf da A’ishatu Ibrahim da ’ya’ya 9, kuma ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa na mutanen Indiya da ake kira Primus da ke Abuja, kuma an yi jana’izarsa a ranar Asabar 27 ga Satumba a garinsa na haihuwa Zariya bisa koyarwar addinin Musulunci. Allah Ya jikansa da gafara Ya sa mu cika da imani idan tamu ta zo.