✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manufar kungiyar ADSI taimaka wa Arewa – Hajiya Khuraira

Sakamakon yadda ake kokawa a kan yadda matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa ke kara tabarbarewa a yankin Arewacin Najeriya, hakan ya zaburar da wasu…

Sakamakon yadda ake kokawa a kan yadda matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa ke kara tabarbarewa a yankin Arewacin Najeriya, hakan ya zaburar da wasu mata kokarin kafa kungiyoyin taimaka wa al’aummar yankin musamman ma mata da kananan yara marasa galihu ta hanyar kafa wata kungiya mai suna ‘Arewa Debelopment Support Initiatibe’ (ADSI). Aminiya ta samu damar tattaunawa da Hajiya Huraira Musa, wadda ta kafa kungiyar, wacce kuma ‘yar Najeriya da ke zaune a Amurka. Ga yadda tattaunawar ta kasance.

Mene ne manufar kafa ADSI

Ba ka ga yadda yanzu ba ka iya tafiya daga Abuja zuwa kaduna ba wani bai tsare ka ba. Yaushe arewa ta zama haka? Yara ba sa zuwa makaranta, kuma ko sun gama makarantar ma babu aiki. Kowa yana jira sai gwamnati ta ba su aiki. To shi ne yanzu mu ka zo mu ka hada kai yadda za mu taimakawa wajen kawo ababuwan cigaba, ta yadda ba sai mun jira gwamnati ta yi mana komai ba. Kamar harkokin kanikanci da makamashin rana, za a iya taimakawa mata su rinka sayarwa a gidajensu. Sannan kuma muna tunanin koyawa matan aure irin ababuwan fasahar sadarwa, ta yadda za su iya yiwa kamfanoni aiki ba sai sun fita daga gidajensu ba.

Ta yaya za ku yi ku cin ma haka?

To yanzu yadda muka yi muka fara shi ne kowane mutum da zai zama dan kungiyarmu, dole ya zama na zai bada kudi Naira dubu biyu kowane wata. A arewa yanzu yawanmu yakai wajen miliyan 100. To a kowace jihar arewa muna son mu samu mutum dubu daya kawai da za su na bayar da Naira dubu biyu kawai. A arewa kawai muna ganin samun miliyan biyu. To miliyan biyun nan ka na ganin Naira dubu biyun nan kamar ba komai ba ne, amma ka yi tunanin miliyan biyun nan kowa ya kawo Naira dubu bibbiyu. Za ka iya taimakon yara mu ba su abin hannunsu, a ba su jari, sannan a gyara makarantu da kuma asibitoci.

Amma kuna ganin abu ne mai yiwuwa a samu wadanda za su tara irin wadannan kudade, ganin akwai talauci da rashin aikin yi a Arewa?

Kana so ka ce yanzu a duk fadin jihar Kaduna ba za mu samu mutane dubu daya da za su bayar da Naira dubu biyu kawai? Ina tambayar ka ne kawai. Sannan mu samu wasu dubu dayan a wata jihar. Babu yadda za a ce hakan ba mai yiwuwa ba. Dole ne mu fara kishin kanmu, mu koma yadda arewa ta ke a da. Yadda da kowa yake taimakawa juna, yanzu kowa ya kama gabansa ne kawai.

Ana zargin kungiyoyi irin naku da kamar neman ci da gumin mutane, ana zuwa ana neman kudi.  Ku shugabanni ko kuma membobi kamar zai muku hanyoyin samun mukamai?

To ka san wani abu, bawai yabon kai ba, mu da muka hadu mu ka kafa kungiyar, kowa na tsaye da kafufunshi. Muna da daidai gwargwado abinda mu ke da shi a hannunmu. Illa dai kawai muna tausayin abin da ke faruwa a arewa, kuma muna neman mutane ire-irenmu su fito su goyi bayanmu, tunanin da muke so mu kawo kenan.

Amma me ya sa sai yanzu kuka ga bukatar ku zo ku kawo irin wannan gudummawa, kasancewar tun da akwai irin wadannan matsalolin?

Tunanin in kawo wannan abin, ya na nan a raina tun shekaru biyar da suka wuce. Amma wani lokacin sai ka hadu da irin wasu mutane, za ku fara sai ka ga hankalinku ba daya bane. Kuma yanzu ababuwan dake faruwan sun yi yawa, babu yanda za a yi kai dan arewa ne ka ga abinda ke faruwa a telebijin ko a hanya kace zaka zauna ka kwanta ka yi bacci ka ce ba wata damuwa. Kuma in ba mu tashi yanzu muka yi wani abu ba, muna ganin suna tsare mu a hanya, to wallahi za su shigo gidajenmu su kakkashe mu. Wannan shi ne gaskiyar al’amari.