Manufofin gwamnati na fifita ’yan kwangilar  waje na cutar da mu – Kwamarade Hamza

Kwamarade Hamza
Kwamarade Hamza

Masu ayyukan gini a Abuja sun jima suna korafin cewa wasu manufofin Gwamnatin Tarayya na jawo musu koma-baya a ayyukansu. Aminiya ta zanta da Shugababan Masu Fasa Duwatsu da Debo Yashi na Kasa, Kwamred Hamza Muhammad inda ya yi bayani a kan lamarin:

A baya Ma’aikatar Babban Birnin Tarayya ta sa dokar hana fasa duwatsu bayan matsalar karamar girgizar kasa, shin yaya lamura suke a yanzu?

An sa wannan doka ce a watan Satumban bara, kuma dokar ta ci gaba har zuwa watan Janairun bana. Hakika al’amura sun yi wa mambobinmu tsauri a lokacin. Kamar yadda ka sani wannan kungiya ta kunshi duk wani aiki da ya shafi tonon wani abu a karkashin kasa ciki har da duwatsu da yashi da sauran ma’adinai sai kuma wadanda ke aikin safara ko alkinta su. Wadansu da suka mallaki motocin aiki a cikinmu kamar tifa da gireda sun saya ne bayan ritaya daga aikin gwamnati, kuma ta nan ne suka rike iyali da sauran hidima.

Me kake jin ya jawo karancin ayyukan ginin da suka shafi yashi da duwatsu?

Dalilan suna da yawa kuma manufofin wannan gwamnati mai ci ne suka haddasa. A baya ministocin Abuja misali kamar El-Rufa’i sun yi kokari wajen kirkiro sababbin gundumomi tare da aiwatar da ayyukan raya kasa kamar na tituna a wurare daban-daban,  sabanin Ministan yanzu wanda ya takaita nasa a aikin a cikin kwaryar birnin Abuja. A zamanin El-Rufa’i ne aka fara aikin gina sababbin matsugunnan ’yan asalin Abuja a Shere da Apo da Kuje da Karshi da sauransu da kuma aikin gina Babbar Kasuwar Abuja da ke Deidei, hakan ya taimaka wajen habakar ayyukanmu. Bayan ya sauka abubuwa sun ja baya.

ADVERTISEMENT

Sai kuma wata matsalar, tsarin wannan gwamnati wajen ba da ayyukan kwangila, domin ba ta tafiya da kananan ’yan kwangila na kasa kamar yadda take tafiya da na kamfunonin waje musamman a fuskar aikin titi da sauransu, alhali kuma wadannan kamfanonin gida sun fi sa kudi ya yi yawo a tsakanin al’umma saboda suna hulda da jama’a a bangarori daban-daban wajen aikin, wadanda ake kira sub-contractors. Da wannan nake kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbata ya zabi ministocin da suka san aiki da kuma kishin al’umma ba wadanda za su zo su maimaita irin kura-kuran da wadansu daga cikin ministocinsa na yanzu suke yi ba. Kamfni irin na China har leburorin ma ’yan fursunan kasarsu suke daukowa su yi musu aiki. A baya mambobinmu na da manyan motoci na tifa da gireda da suka zarce 500, amma yanzu yawanci wasu sun tsaya ba kuma zarafin maye gurbinsu da sababbi saboda ba ayyuka, wadansu mambobin kuma sun ma dauke motocin daga nan Abuja sun koma da su zuwa jihohi.

Ba ka ganin dogewar gwamnati na sai wadanda ke da kwarewar aiki da kayan aiki ne ya sa wasu kamfanonin gidan ba sa samun aikin?

Bin diddigi ba laifi ba ne, inda matsalar take ita ce nuna son kai a wajen masu ba da aikin. Misali guda da zan ba ka wannan tsari da ake kira “Due process” a Turance gwamnatin Obasanjo ce ta kirkiro shi don cimma wata manufa, kuma hakika ya cimma burinsa. Saboda a lokacin akwai al’ummar Arewa da dama da ke ayyukan kwangilar gina gidaje a manyan biranen kasar nan, suna da duk nau’o’in motocin aiki. Sai dai kasancewa yawancin jagororin masu kamfanin ba injiniyoyi ba ne, idan aka gayyaci kamfani ya zo ya yi bayani a kan tsarin aiki kafin a tabbatar masa da kwangila, dole sai dai ya tura wani injiniya ya wakilce shi, shi ke nan daga nan sai ya koma kamar shi ne mai gida a wajen gwamnati. Zuwa wani lokaci sai shi ma ya yi rajista ya zama shi ne ake bai wa aikin. Alhali kuma su masu wadannan kamfanoni na hakika wadanda yawanci ’yan Arewa ne da suka jima suna wadannan ayyuka, suna aikin gini mai inganci. Su kuwa injiniyoyin nan sai a samu wani ya yi aiki na ha’inci bayan wani lokaci ka ji gini ya rushe kamar yadda yake ta faruwa a yanzu. To ta haka mutanenmu da dama suna ji suna gani suka rasa ayyuka, su kuma wadancan suka maye gurbinsu.

Akwai masu cewa rashin samun damar satar kudin gwamnati da gwamnatin yanzu ta takaita shi ne ya sa aikin gini ya ja baya?

Akwai wannan, sai dai abin da nake so ka sani wannan ba zai zama babban dalili ba. Tun a lokacin gwamnatin Obasanjo ne bayan gwamnatinsa ta gwanjatar da gidajen da gwamnatoci suka gina a baya, sai ta dakatar da daukar nauyin gina gida daga bangaren gwamnati wanda al’umma suka yi nisa wajen cin gajiyar ayyukan. Daga lokacin ne kamfanoni suka shiga lamarin ba wai masu satar kudin gwamnati kadai ba kamar yadda wadansu ke fada. To sai dai abin da ke faruwa a yanzu shi ne Ma’aikatar Babbar Birnin Tarayya, Abuja kusan ta jingine kirkiro sababbin gundumomi ko kai ayyukan raya kasa wajen birnin.

A karshe wace shawara za ka ba gwamnatin wajen farfado da masana’antu?

Babbar shawarata ga gwamnati ita ce ta yi dukkan mai yiwuwa wajen ganin ta karasa aikin Kamfanin Karafa na Ajaokuta. Waje ne da aka tsara zai samar da dimbin ayyuka ga masana’antu ba kawai daidaikun jama’a ba. Dukkan nau’o’in kamfanonin da ke da nasaba da karfe na bukatar karfe a wajensu wanda za su samar daga ma’adinai da ake haka a wajen. Ayyukan masana’antar zai sa a samu kamfanoni masu yawa da kuma kawo karshen shigo da karafa sai ma a fitar zuwa waje don sama wa kasa kudi a wasu bangarori a maimakon dogaro da bangaren mai kadai kamar yadda ke faruwa a yanzu.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya