Daily Trust Aminiya - Manyan fina-finan Kannywood 5 na bara da za su fito bana
Subscribe

Manyan fina-finan Kannywood 5 na bara da za su fito bana

Kamar yadda aka sani, Masana’antar Kannywood ta dan samu tsaiko musamman a bara kasancewar tabarbarewar tattalin arzikin masana’antar.

Furudusushi da dama sun koma gefe sun yi shiru, wasu kuma sun koma wasu harkar.

Akwai fina-finai da dama da aka shirya a bara, amma tsoron asara ya sa masu fina-finan suka ajiye su a gefe.

Don haka ne Aminiya ta rairayo wasu fina-finan bara, da za a sake su a kwanan nan, kuma aka riga aka saki a bana.

Mati a Zazzau

Fim din Mati a Zazzau mutane da dama sun dade suna tsimayinsa, musamman ganin cewa ya zo da sabun abu, ciki har da kasancewar sabuwar jaruma, wadda fitacciyar mawakiya ce ta Hip-Hop, amma ’yar asalin Arewa wato Dija.

Kamfanin Sadau Pictures Production ne ya dauki nauyin fim, kuma Rahama Sadau da Sadiq Sani Sadiq suka dauki nauyi, sannan Yaseen Auwal ya bada umarni.

Hoto: Instgaram na Rahama Sadau

Karshen Tika Tiki

Halima Atete ce ta dauki nauyin fim din Karshen Tika Tiki, sannan darakta Sheikh Isa Alolo ne ya tsara kuma ya bda umarnin fim din.

Akwai jarumai irinsu Ali Nuhu da Shuaibu Lawal Kumurci da sauransu. An dauki fim din a bara, amma za a fara haske shi ne a wannan watan na Janairu.

Hoto: Instagram na Ali Nuhu

Bin Ali

Fim din Bin Ali, wanda kamfanin Abdul Amart Mai Kwasewa wato Abnur Entertainment ya dauki nauyi akwai jarumi Ali Nuhu da danda Ahmad Ali Nuhu.

Darakta Sadik N. Mafiya ne bada umarni. Shi ma an dauke shi ne bara, amma za a sha kallo a bana.

Hoto: Instagram na Ali Nuhu

Dafin So

Shi ma Dafin So, kamfanin Abnur ne ya dauki nauyi, kuma akwai jarumi Adam A. Zango da jaruma A’isha Tsamiya, sannan darakta Sadik N. Mafiya ya bada umarni.

Hoto: Instgram na Abdul Amart

Karamin Sani

Karamin Sani fim ne da darakta Falalu Dorayi ya bada umarni, kuma yanzu haka an fara nuna shi a sinima a Kano.

Hoto: Instgram na Falalu Dorayi
texem
More Stories