✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan jami’an soji har yanzu suna biyayya ga Al-Bashir – Rayyan Adam

Rayyan Adam, daya ce daga cikin matasan kasar Sudan da ke gaba-gaba wajen gudanar da zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin Omar al-Bashir, kuma a…

Rayyan Adam, daya ce daga cikin matasan kasar Sudan da ke gaba-gaba wajen gudanar da zanga-zangar da ta kifar da gwamnatin Omar al-Bashir, kuma a halin yanzu take kiran da lallai sojojin su mika mulki ga farar hula. Rayyan, wadda likita ce da ke aiki a asibitin ’yan sandan kasar-ta bayyana mana dalilin shigar ta zanga-zangar da kuma fatan da take da shi ga kasar.

Me nene ya tunzura ki wajen shiga zanga-zangar?

Rashin ayyukan yi da karancin albashi, sa’annan babu kayan aiki tare da gurbacewar harkar kiwon lafiya  a kasar Sudan. Amma ga Amro wanda shi ya kasance mai shelar zanga-zangar; kuma kani ne a wurina. Akwai rashin kudade tare da rashin albashi ga ma’aikatan lafiya tun watan Satumba, kuma akwai hauhawar farashin ababen da sai da su rayuwa ke gudana.

Mene ne takamaiman aikin da ki ka yi a zanga-zangar?

Na kasance cikin masu zanga-zangar tun ranar 6 ga watan Afrilu, har zuwa ranar 12 ga watan, tare da wasu mata uku, wanda su ma suka shiga zanga-zangar. Aikina ciki, shi ne na shiga macin tun daga karfe 7 na yamma zuwa 12n dare.

Ganin cewa yanzu Shugaba al-Bashir ya kau daga karaga, me kike hange game da makomar Sudan?

Da irin wannan mulkin shekaru 30, a yanzu ina fatan Sudan ta kome kan tafarkin dimokradiyya-inda zan fadi abin da ke raina, kuma na sanya irin tufar da na ke so, ake kuma wanzar da adalci ga kowa. Ina kuma fatan Sudan ta zama kasar da take da daidaiton tattalin arziki da tsaro tare da kyakkyawan niyyar yin gyaran fuska daga dukkanin masu ruwa da tsaki a kasar.

Ko kina ganin hambarar da al-Bashir daga mulki zai warware matsalolin kasar? 

Tabbas! Shugaba Bashir dan kama-karya ne kuma mai cike da cin hanci da rashawa. Ya zama dan ina da kisan kare dangi. Amma muna addu’ar Allah sa makomar kasar ta zama mai kyau, sakamakon tumbuke shi da kuma kawar da gwamnatinsa.

Ko kin damu da yadda har yanzu wasu magoya bayansa ke ci gaba da rike mukamai kuma suke damawa a mulkin kasar?

Eh, kwarai kuwa. Wannan ne dalilin da ya sa muka hambare babban na hannun damansa, Ibn Ouf, sa’o’I 24 bayan kifar da gwamnatin al-Bashir.

Ko kun damu, musamman ma matasan Sudan, a kan yiyuwar maimata irin abin da ya faru a kasashen Masar da Libya bayan kifar da gwamnatocin Shugaba Mubarak da kuma Ghaddafi, kwatankwacin yanayin ya faru ga kasarku, Sudan?

Abin da ke faruwa a kan tituna, yana nuni ga yiwuwar Sudan ta zama kamar Libya ko Masar, shi ne karamin abin da muke da damuwa a kai.  Ko da manyan kwamandojin sojan da suke dafawa matasa masu zanga-zangar, sun kare gwamnatin ta hanyar hambarar da Omar al-Bashir. Muna kiran su Kizan. Har yanzu da akwai gungun wadannan sojojin dake biyayya ga Omar al-Bashir, suna tafiyar da mulkin kasar a karkashin salon mulki irin na soji.

Ko za ki iya bayyana mana wani labari na ki ko na wani danginki na kusa game da irin wahalhalun da kuka jure wa a lokacin mulkin Shugaba al-Bashir kuma ya aka yi har kuka ga karshen abin?

An kama tare da kulle kawata, sa’annan wasu tsageru uku suka yi mata fyade; kawai don ta saka wando da kuma tafiya tare da dan uwanta, wanda suka yi zaton farkanta ne. Dukkaninsu an kulle su, ita kuma aka yi mata fyade. Budurwa ce har yanzu da na ke magana da ke, amma dukkan su sun bar kasar. Mutanen da suka aikata wannan danyen aikin, suna nan suna yawonsu, ba tare da an hukunta sub a. Babu adalci, sam.

Kin taba yunkurin yin wata zanga-zanga makamanciyar wannan, a lokacin juyin juya halin kasashen Larabawa amma abin ya faskara, me yasa?

Mun gaza, sakamakon yadda a wancan lokacin mutane ke fargabar sojoji: sai dai a yanzu muna tare da sojojin; inda suke dafa mana.

Ta yaya kuka samu nasarar kiran ’yan Sudan da su fito su shiga zanga-zangar?

Ta hanyar kafofin sada zumunta na zamani. Mutane na bukatar da ilmantar da su sosai da sosai a kan halin siyasar kasar. Muna rayuwa a kasa mai bambamcen kabilu; da kusan kullum su ke mujadala da juna. Ko da yake, anan kam, ra’ayinmu ya zo daya game da wancan bakin mulkin; da kuma bukatar mu hadu wajen kawar da shi.

Da akwai bayanai masu cin karo da juna, dangane da aihinin abin da ya haifar da zanga-zangar tun farko. Daga batun karin farashi a kan burodi da dai sauransu. Me nene takamamman dalilin faro zanga-zangar?

Eh, duka wadannan dalilan da aka ambata, sun kasance suna faruwa a lokaci. ’Yan kasar Sudan, sun kasance masu matukar juriya da hakuri. Ko da yake lalata tattalin arziki tare da mummunan hauhawar farashi, cikin kankanin lokaci, sun kai su tunzura mutane wajen yin zanga-zanga. Dalilan da yawa, akwai rashin kudade a hannun jama’a da rage darajar takaddar kudin kasar da tashin farashin makamashi da na burodi da ma kayan masarufi da dai sauransu da dama.

Ki bayyana ko ya kika ji, a sa’ilin da aka ce an tumbuke al-Bashir daga karagar mulki?

A gaskiya mun kasance cikin kaduwa. Abin ya zo mana tamkar a mafarki, tare da sosa rai da hawayen godiyar samun waraka. Abin tarihi ne sosai, wanda ya sauya alkiblar kasar wajen zama tsintsiya madaurinki daya. An dai yi abin tarihi; kuma kasancewa cikin abin tarihin, muhimmin abu ne a rayuwa. A kashin kaina, abin ya sosa min rai.

Lokacin da aka faro zanga-zangar, ko kin yi hasashen samun juyin mulki?

A zancen gaskiya, tun da jimawa ta bayyana cewa gwamnatin a rabe take. Duk wanda ya bayyana ra’ayinsa ko dai a kore shi daga bakin aiki ko kuma ma a garkame shi a kurkuku. Juyin mulkin shi ne kawai mafita ga wannan gwamnatin da ta share shekaru 30 kan gadon mulki, za ta fadi.