✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan jami’an tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma 200 suka kalli fim din Juyin Sarauta a Abuja

Manyan jami’an hukumomin tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma su 200 a karkashin jagorancin Hadiza Bala Usman, Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya…

Manyan jami’an hukumomin tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma su 200 a karkashin jagorancin Hadiza Bala Usman, Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA) da fitattun marubuta da ’yan jarida da ’yan fim suka kalli fim din Juyin Sarauta a gidan fim din zamani na Silberbird da ke Abuja, Babban Birnin Najeriya.

Nuna fim din ya biyo bayan bukatar da Hadiza Bala Usman ta bijiro wa Kamfanin Ramat Production, wanda ya shirya Juyin Sarauta lokacin da aka gayyace ta kaddamar da fim din, inda shugabar ta fifita bukatar ganin dimbin al’umma daga Afirka ta Yamma sun amfana da fim din mai nuna tarihi da al’ada kan yadda ake gudanar da harkokin sarauta a tsawon zamanin rayuwar Bahaushe.

Fim din Juyin Sarauta ya kasance irinsa na Hausa na farko da ya zama zakaran gwajin dafi wanda kuma ya taba shiga gasar fina-finai ta duniya ta Lake International Pan African Film Festibal da ake gudanarwa shekara-shekara a kasar Kenya, kuma an fitar da shi a jerin zakarun da za su fafata a gasar ranar 7 zuwa 10 ga  Nuwamban bana. Sannan ya kasance a jerin fina-finan da za su fafata a gasar nagartattun fina-finai a nan gida Najeriya, wato Kaduna Film Festibal, wadda za a gudanar a Kaduna ranar 25-27 ga watan nan.

Tun cikin shekarar 2017 fim din Juyin Sarauta ya lashe gasar Zuma Film Festibal, Abuja a matsayin fim din da ya fi kowane fim da aka yi da harshen gida Najeriya (Best Nigerian Language Film), sannan a bana ya lashe kyaututtuka 6 a gasar AMMA.

Shugabar Kamfanin Ramat Production, da ya dauki nauyin shiryawa da dawainiyarsa, Balaraba Ramat Yakub, ta yi fatan ganin da zarar fitowar Juyin Sarauta kasuwa ya samu karbuwa don amfanin al’umma, musamman masu nazarin adabin Hausa a jami’o’i da manyan makarantun kasar nan.

Aminiya ta tattauna da Manajan Daraktar Hukumar NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman, jim kada da kammala nuna fim din, inda ta ce:

“Wannan shiri ya burge ni kwarai, ya nuna mana yadda zamantakewa take a cikin gida tsakanin mata, yadda kishi ke sanya mu kashe kanmu, mu lalata wa ’ya’yanmu rayuwa, duk a gwagwarmayar neman sarauta. Muna kira ga mutane su kalli fim din. Duk da cewa ba a wannan zamanin ne abin da ke cikin fim din ya faru ba amma ko a yanzu abubuwa makamancinsu suna faruwa. Wannan darasi ne gare mu iyaye kuma darasi ne gare mu mata, darasi ne ga al’amarin fuskantar shugabanci da al’amarin mulki.”

Kan za ta iya kwatanta shi da yanayin mulkin dimokuradiyya na yanzu? Sai ta ce, “Mulki kowane iri ne, na sarauta ko na dimokuradiyya duk yana tafiya da fannin suka da fannin lalaci ko yadda ake kokarin lalata mutum duk da cewa ba mutumin banza ba ne, saboda son kai, don kawai mutum na son fifita kansa a kan wani… Don haka lallai duk abin da ka gani a fim din nan, za ka iya ganinsa ko a yau a cikin dimokuradiyya ko a cikin gidajenmu na sarauta, za ka ga na faruwa ko a yau.”

Yawancin fina-finan Hausa suna ta’allaka da zamani, amma ganin cewa fim din Juyin Sarauta cike yake da al’amuran gargajiya da al’adar Bahaushe, Hadiza Bala Usman ta ce:

“Wannan ci gaba ne ga fina-finanmu, musamman idan aka yi la’akari da yadda aka koma shekarun baya da suka wuce, wannan ya gwada cewa akwai kwarewa, akwai maganar tarihi, an je baya an duba tarihi yadda masarautunmu suke a lokacin kuma ya nuna wa yaranmu wadanda ba su sani ba su sani cewa ga yadda zamanin baya yake, sanadiyyar wannan fim sun ga yadda abin yake a can baya. Alhamdu lillahi, ya burge ni kawarai.”

Jagororin fim din Juyin Sarauta, sun bayyana wa Aminiya yadda suka shirya fim din da nasara ko kalubale da suka gamu da su. Ado Ahmad Gidan Dabino, jarumin fim din kuma daya daga cikin wadanda suka shirya shi ya ce fitowar fim din da nasarorin da ya samu kuma yake kan samu babbar nasara ce.

“Wannan fim shi ne fim din Hausa na farko da aka taba nunawa a wannan babban gidan nuna fim na zamani na Silberbird, Abuja,” inji Ado.

“Tun farko mun yi la’akari cewa al’mummar Hausa na bukatar ta nuna kanta da asalinta a wannan zamani. Dalili ke nan ya sanya muka zabi mu shirya wannan fim, wanda ya waiga baya kan yadda al’amuran sarauta suke, shekara 100 da suka gabata. Mun shirya komai a gargajiyance kuma a al’adance. Wannan ya hada da tsarin gidan sarauta da garin wanda muka gina shi da kanmu bisa tsarin da ya dace da yanayin shekara 100 da suka gabata.”

Ya yi kira ga abokan sana’arsa cewa ya kamata su maida hankali sosai wajen shirya fina-finan da suka dace da rayuwa da al’adun Hausa, maimakon kwaikwayon na Indiya da Amurka. Ya ce, “Babu yadda za ka nuna al’adar Bahaushe ta hanyar kwaikwayon al’adun Indiya da Turawa. Su kansu kasashen Turawan, sun fi sha’awar su ga fim din da aka shirya a gargajiyance, wanda ke nuna al’adun da ba nasu ba. Babu yadda za ka burge Bature ta hanyar nuna masa dogayen gine-gine ko motar zamani da sauransu.”

Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, wadda ta rubuta labarin fim din kuma ta shirya shi. Ta ce a baya ta shirya fina-finai biyu da suka hada da ‘Sai A Lahira’ da Ina Sonsa Haka’ sai wannan na Juyin Sarauta na uku.

“Babu shakka mun sha wahala wajen tara kudin da muka shirya wannan fim na Juyin Sarauta, inda ya hada da cin bashi daga banki da sauransu. Amma muna da yakinin cewa da taimakon Allah za mu fita kuma za mu ci gaba da shirya wasu fina-finan makamancinsa,” inji ta.

Kan tallata fim din kuwa, ta ce: “Babban kalubalen da ke ci mana tuwo a kwarya shi ne na barayin fasaha, don haka ina kira ga jama’a su tabbatar sun sayi fim din nan idan ya shiga kasuwa. Za mu ci gaba da kokarin tallata shi a gida da waje kuma muna godiya ga Allah da Ya ba mu nasara, ganin cewa tun yanzu fim dinmu ya ci gasa iri-iri har shida kuma muna sa ran ya ci gaba da samun nasara a duniya.”

Isa Adam, daya daga cikin jaruman fim din, ya bayyana jin dadinsa kan yadda ya samu damar fitowa a fim din da ya kira da cewa muhimmi ne da ya bambanta da sauran fina-finan Hausa. Ya bayyana kalubalen da ya fuskanta lokacin da ya rika koyon Karin Hausar Sakkwatanci, domin ta dace da fim din.

Falalu Abubakar dorayi ne Daraktan da ya ba da umarni a fim din Juyin Sarauta, ya bayyana fim din da zakaran gwajin dafin nuna al’adun Hausawa ga duniya.

“Da aka ba ni daftarin labarin fim din, na nazarce shi sannan na yi ’yan gyare-gyare a cikinsa yadda za a kauce muzanta masarautunmu. Haka mun nemi shawarwari daga kwararru da suka san sarautar gargajiyar Bahaushe. Misali, akwai wata tsohuwa wacce ta haura shekara 80 a duniya, wacce masaniya ce na yadda ake tafiyar da rayuwa a gidajen sarauta, ta taimaka mana sosai da shawarwari wajen tafiyar da fim din,” inji Darakta  dorayi.