✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan makarantu za su fara daukar dalibai daga 21 ga watan Agusta – JAMB

Za a bayar da guraben ne ga daliban da suka nema a matsayin zabi na daya da na biyu.,

Hukumar kula da Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta umarci makarantun da su fara bayar da gurabe ga dalibai a zangon karatu na 2020/2021 daga ranar 21 ga watan Agusta.

Hakan na kunshe ne a cikin wani kundin ka’idojin bayar da guraben na bana da kakakin JAMB, Fabian Benjamin ya fitar ga shugabannin manyan makarantun a ranar Lahadi.

JAMB ta kuma umarci makarantun da su wallafa sunayen sabbin daliban da suka sami guraben a shafinta da ma na sauran hukumomin da ke da alhaki, tana mai jan kunnensu da kada su kuskura su sayar ko tallata guraben.

Hukumar ta ce, “Makarantun za su fara bayar da guraben ne ga daliban da suka nema a matsayin zabi na daya da na biyu, daga 21 ga watan Agusta har zuwa lokacin da Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya za ta kayyade a nan gaba.

Ta ce ta saka lokacin ne saboda rashin tabbas da ake fama da shi a bana saboda annobar COVID-19.

Kazalika, JAMB ta gargadi makarantun da kada su karbi sama da Naira 2,000 daga hannun dalibai a matsayin kudin jarrabawar Post-UTME.