Da Dumi Dumi

Manyan ‘yan sanda 11 sun samu karin girma a Jihar Oyo

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Oyo, Mista Shina Olukolu ya gargadi manyan jami’an ’yan sanda 11 da suka samu karin girma a jihar cewa, su sani wasu kura-kurai da suka yi a baya aka yafe musu ba za a yafe irin wadannan kura-kurai a yanzu da kuka samu karin girma ba.

Kwamishina Olukolu ya ce “Karin girman da aka yi muku yana bukatar kishin kasa da kara jajircewa da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukan tsaro domin ku zama abin koyi ga na baya.”

Mista Shina Olukolu, ya fadi haka ne a ranar Litinin da ta gabata lokacin da yake lika karin girman da jami’an suka samu a wajen bikin makala musu girman a Hedkwatar ’Yan sandan da ke Eleyele a Ibadan.

Mataimakin Kwamishinan ’Yan sanda Attahiru Isa ne ya taimaka wa Kwamishina Shina Olukolu wajen makala mukaman karin girman a gaban manyan jami’an da suka halarci taron.

ADVERTISEMENT
Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya