Da Dumi Dumi

Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano

Masu bibiyar wannan fili na Iyayen Giji kamar kullum ina yi muku gaisuwa irin ta Musulunci, assalamu alaikum. Da fatan kuna cikin koshin lafiya. Marasa lafiya kuma Allah Ya ba su lafiya sannan wadanda suke cikin mummunan yanayi Allah Ya yaye musu. Wadanda suka rasu Allah Ya jikansu da rahama.  Mu kuma da muka rage Allah Ya ba mu ikon cikawa da imani.  Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya.  Allah Ya kawo mana karshen fitintinun da suke damun wannan kasa tamu.

A yau zan tabo wani muhimmin batu ne da ke ci wa al’ummarmu tuwo a kwarya musamman al’ummar Arewa. Wannan batu shi ne na yawan sakin aure da wadansu suka mayar tamkar  sanya riga  da safe sannan su tube ta da yamma.

Al’amarin aure ya fi karfin wasa, shi ya sa addini ya hori maza da mata su yi kyakkyawan bincike a kan juna kafin su auri juna.

Sai dai bincike ya nuna daga cikin matsalolin da ke tattare da aure a nan Arewa akwai jahilci da son rai da son abin duniya da kuma neman mallakar dukiyar miji ko ta mace idan daya daga ciki ya rasu.

Saboda matsalar yawan sakin aure da ke addabar wasu jihohi da ke Arewa ne ya sa wasu gwamnoni da shugabanni suka fara tunanin hanyoyin da suka kamata a bi don a shawo kan lamarin.  Daga cikin wadannan gwamnoni, akwai Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje.

ADVERTISEMENT

A kwanakin baya ne Gwamnan ya nemi Majalisar Dokokin Jihar ta samar da wata doka da za ta rika tilasta duk magidancin da ya saki matarsa biyan diyya ga matar.  Kamar yadda rahoton ya nuna, duk magidancin da ya kuskura ya rabu da matarsa ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, to zai biya matar diyya ko ya ci gaba da daukar nauyinta da na ’ya’yan da suka haifa  har tsawon lokacin da za ta sake yin wani auren.  Sannan daga nan dole ya ci gaba da daukar nauyin ’ya’yansa har su girma.

Gwamnan ya nuna takaici kan yadda wadansu magidanta sukan saki matansu bayan sun shafe fiye da shekara 30 zuwa sama suna tare da juna amma a kan abin da bai taka kara ya karya ba sai su sake su.  A wannan lokaci girma ya kama matar inda da wuya ta samu wani mijin da za ta sake aura yayin da mijin zai iya auren budurwa.

Abin ba ga tsofaffi kurum ya tsaya ba. Bincike ya nuna akwai matar da aka aura kuma aka sake ta a kasa da mako biyu.  Da jin haka ka san akwai rashin hankali ko rashin tunani.  Ta yaya mutum zai bata lokaci ya auri mace amma ya rabu da ita a kasa da mako biyu?  Wani zai iya cewa watakila laifin daga wajen amaryar yake.  To abin tambaya a nan shi ne, me ya sa addinin ya nemi a yi bincike kafin aure?

 

Za mu ci gaba

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya