Da Dumi Dumi

Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano(3)

A ci gaba da tattauna wannan maudu’i mai take a sama a yau zan karkata akalata ce zuwa bangaren kura-kuren da wadansu mata suke yi kamar yadda na yi alkawari, wanda hakan ke sanya maza ke sakinsu a mafi yawan lokuta.

Ga wasu daga cikin dalilan da ke sanya wadansu maza ke sakin matansu.

Akwai rahoton da ya nuna yadda wata mata da ba ta yi wa mijinta biyayya, duk da sun yi auren soyayya  amma  saboda zugar wadansu  kawaye sai ta canja wa mijin ba gaira, ba dalili.   Duk abin da ya umarci ta yi masa a zamantakewar aure to ita akasin haka za ta yi da gangan, ba bisa kuskure ba.  Tun mijin yana hakuri har ta kai ya kai kararta wurin magabata amma duk da haka ba ta daina ba. Abin yana matukar tayar masa da hankali, don ko gida ba ya son ya koma da wuri idan ya tashi daga kasuwa. Yakan wuce wajen abokansa ne su yi ta hira har sai dare ya fara nisa sannan ya lallaba ya koma gida ya kwanta kamar wani mara gaskiya. Da gari ya waye sai ya bar gidan saboda rashin sukuni.  Hasali ma a kasuwa yake karyawa duk da yana da mace a gida. Ita kuwa ko a jikinta. Ba wannan magidanci kadai ba, na tabbata akwai maza da dama da suke fuskantar irin wannan yanayi a gidajensu na aure.

Rahoton ya nuna  cewa wata rana kafin ya fita kasuwa sai ya ajiye mata kudin cefane daidai gwargwado kamar yadda ya saba.  Ashe ba tare da saninsa ba da zarar ya fita, sai ita ma ta fita unguwa ba tare da izininsa ba.

Ran nan matar ta fita unguwa ba tare da sanin mijin ba kamar yadda ta saba, sai ta yi hadari a kan babur din acaba tare da wata ’yarsu da ba ta wuce shekara biyu ba.  Matar da ’yar suka ji mummunan rauni mai tayar da hankali.   Sun fada cikin wani rami ne da hakan ya sa suka ji mummunan rauni. Nan jama’a suka taru aka taimaka za a kai su wani asibiti mafi kusa.  Cikin ikon Allah wani makwabcinsu ya je wucewa sai ya ga jama’a sun taru a wajen da aka yi hadarin. Da ya lura da kyau sai ya gane matar makabcinsa ne, inda nan take ya buga masa waya ya sanar da shi halin da ake ciki. Nan take mijin ya nufi asibitin da aka kai matar da ’yarsa.  Ya biya kudin yi musu magani, bayan an sallame su sun koma gida ne sai ya nemi matarsa ta koma gidan iyayenta ya sake ta.   Mijin ya nuna rabuwa da ita shi ne mafi alheri a wajensa.

ADVERTISEMENT

Haka kuma wani labari ya nuna yadda wata amarya ba ta barin mijinta ya yi sunna da ita har sai ya ba ta makudan kudi, saboda ta fahimci yana da tsananin sha’awa. Sai ta rika amfani da wannan dama wajen tursasa masa sai ya ba ta  kudi kafin ta amince masa. Ya yi mata nasiha, ya kai kararta wajen magabata amma duk a banza. Da ya fahimci ba ta da niyyar canja hali kuma tana neman ta jefa shi cikin wani mugun hali sai ya kara  wani auren.

Bayan ya kara aure ne sai ta nemi ta tayar masa da hankali da na amaryar. Bai bata lokaci ba sai ya sake ta don kada ta gurbata masa gida. Bayan an sake ta ne sai idonta ya raina fata don ta shafe lokaci mai tsawo ba tare da samun wani miji ba, saboda labarin da aka rika yadawa a kan halinta. Nan dai ta shiga yin nadama a kan abin da ta aikata aka sake ta.

Mu kwana nan

 

Za a iya samun Ahmed Garba Mohammed a 08097015805

 

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya