✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marar hannuwa da take tuka jirgin sama da kafa

Wata marar hannuwa mai suna Jessica Cod, ta cimma burinta a rayuwa inda ta zama direbar jirgin sama ta hanyar tuka shi da kafa. Kadan…

Wata marar hannuwa mai suna Jessica Cod, ta cimma burinta a rayuwa inda ta zama direbar jirgin sama ta hanyar tuka shi da kafa. Kadan daga cikin tarihinta ya nuna: An haifi Jessica a garin Sierra Bista a Jihar Arizona da ke Amurka, kuma ta kammala karatun digirinta a Jami’ar Arizona, sannan ta kafa tarihin zama matukiyar jirgin sama ta farko marar hannuwa.

An haifi Jessica da wannan nakasa ce kuma tana amfani da kafarta ce wajen yin ayyuka da yawa inda ta samu nasarar karbar bakar damara a wasan Taekwondo. Jessica ta taba shiga gasar gudu ta mil 40 da El Tour de Tuscon suka shirya kuma ta rubuta littafi mai suna Disarm Your Limits wato Nakasa ba tawaya ba ce.

Wannan na cikin labarin Jessica Cod kuma yana daya daga cikin labaran da suka tabbatar da haka. Duk da cewa an haife ta babu hannuwa, ba ta taba barin hakan ya nakasa rayuwarta ba. Ta samu nasarar karbar bakar damara a gasar Taekwaondo, kuma tana yin sauran al’amuran rayuwarta kamar yadda masu hannuwa ke yi. Tana iya yin kida da Piano da wasu abubuwan kida. Daga cikin manyan ababen al’ajabi da hazikancin Jessica akwai, zamanta matukiyar jirgin sama ta farko a duniya mara hannuwa.

Jessica ta wallafa cewa, mutane da yawa na kallon rashin hannunta a matsayin nakasa, amma tana son kawar da tunaninsu. Mijinta ya ce zai iya kwatanta ta da dabi’u uku: “Saukin kai, kokari da kuma jarumta.” Jessica ta fara kokarin zama matukiyar jirgin sama ce bayan wani matukin jirgin sama na yaki, ya tunkare ta da batun ko za ta so zama irinsa.