✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marayu da marasa galihu sun yi Sallah cikin walwala a Alabar Rago

Kwamitin Kyautata Rayuwar Jama’a na Msallacin Sheikh Ahmad Saleh da ke Kasuwar Alaba Rago a Legas ya yi wa marayu da marasa galihu goma sha…

Kwamitin Kyautata Rayuwar Jama’a na Msallacin Sheikh Ahmad Saleh da ke Kasuwar Alaba Rago a Legas ya yi wa marayu da marasa galihu goma sha tara ta arziki, inda ya yi musu layya aka yanka musu sa da rago aka rarraba musu naman domin su sami damar yin bikin Sallah tamkar kowa.

Shugaban Kwamitin, Malam Ahmad Saleh ya shaida wa Aminiya cewa lura da yawan marayu da marasa galihu  a yankin sai kwamitin ya yanke shawarar ya kamata a yi musu layya a raba musu naman domin  su yi murnar Sallah tamkar kowa. “Cikin ikon Allah mun samu ikon yi koda ba yawa, kasancewar layya Sunnah ce mai karfi a kan masu hali, amma ciyar da maraya wajibi ne, don haka muka ga bai dace muna cikin murna da walwala ba alhali akwai wadanda ba su da shi a cikinmu, akwai yaran da ba su da iyaye akwai iyayen da ba su da karfi. Da muka bijiro da wannan sai wadansu bayin Allah da ba sa so a ambaci sunansu suka taimaka aka saya musu saniya da rago aka yi musu layya, wannan abu na da matukar tasiri, domin sun yi Sallah cikin walwala, wadanda suka ba da gudunmawar kuma sun samu lada domin saboda Allah suka yi. Mutumin farko da muka bai wa naman dattijo ne mai ’ya’ya shida mun lura cewa shekaru da dama da muka san shi bai taba yin layya ba don haka muka kira shi muka ba shi ka ga yanzun zai kai naman a dafa wa yaransa wannan kadan ne daga cikin tasirin wannan aiki,” inji shi.

Aminiya ta zanta da Malam Abubakar wanda ya wakilci yara marayu uku bayan da aka ba shi rabonsu na naman, inda ya ce yaran da yake wakilta za su yi farin ciki kwarai domin marayu ne da ba su da uba, idan suka ga an kai musu naman za su tabbatar wadansu ne suka tuna da su suka taimaka musu, “Taimakon maraya taimakon kai ne, domin yi wa dan wani yi wa naka ne, idan an je da kai an rufe dan uwanka a kabari, kana ganin ’ya’yansa a gabanka to ka taimake su domin kai ma wata rana ’ya’yanka za su zama marayu a gaban wani. In ka taimaki marayun wani kai ma sai Allah Ya kawo wadanda za su taimaki naka,” inji shi.

Wani dattijo mai suna Umar Direba ya bayyana wa Aminiya farin cikinsa, inda ya ce ’ya’yansa shida, ya yi farin cikin samun abin da zai kai musu su dafa su ci a ranar Sallah. “Muna yi musu addu’ar Allah Ya saka musu,  mu ma Ya ba mu ikon yin makamancin haka, shugabanninmu Allah Ya sa adalci a zukatansu Ya yi musu jagora Ya ba mu zaman lafiya Ya yi mana ganin fitunu a kasarmu,” inji shi.

Yara marayu da dama da Aminiya ta zanta da su lokacin da ake raba musu danyen naman layyar a safiyar Lahadin ta gabata sun kasance cikin farin ciki da walwala inda suka ce za su kai naman gida a soya musu su ma su yi bikin Sallar cikin jin dadi.