Da Dumi Dumi

Maroko 2019: Gwamnatin Tarayya ta yi wa ’yan wasa ruwan Dala

A ranar Talatar da ta wuce a Abuja, Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta saka wa ’yan wasan da suka nuna bajinta a Gasar Wasanni ta Afirka da aka yi a Maroko.

Najeriya ce ta biyu a gasar wajen yawan lambobin yabo.

A bikin bayar da kyaututtukan ga ’yan wasan a sansanin horar da ’yan wasa na Games Billage da ke Abuja, Babban Sakataren Ma’aikatar Matasa da Wasanni Mista Olusade Adesola wanda ya wakilci Ministan Matasa da Wasanni Mista Sunday Dare ya karrama ’yan wasa 58 da jami’ansu hudu.

An ba kowane dan wasan da ya samu lambar zinare kyautar Dala dubu uku kimanin Naira miliyan daya da dubu 89 yayin da wadanda suka samu lambar azurfa suka tashi da Dala dubu biyu kimanin Naira dubu 726 sannan wadanda suka samu lambar tagulla sun samu kyautar Dala 1,500 kimanin Naira dubu 544 da 500.

Sannan an ba ’yan kwallon maza da mata Dala dubu 6 kowannensu, kimanin Naira miliyan biyu da dubu 178  yayin da aka ba daukacin ’yan kwallon Badminton Dala dubu 18 kimanin Naira miliyan 6 da dubu 534 don su raba a tsakaninsu.

ADVERTISEMENT

’Yan wasan da jami’ansu sun nuna farin ciki game da karramawar da aka yi musu inda suka sha alwashin ci gaba da nuna bajinta a gasar Olamfik da za a yi badi (2020) a Tokyo na Japan.

 

 

Share