✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maroko 2019: Yau Flying Eagles za ta kece raini da Burkina Faso a wasan karshe

A ci gaba da fafatawa a Gasar Wasanni ta Afirka karo na 12 da ke gudana a kasar Maroko, a yau Juma’a da misalin karfe…

A ci gaba da fafatawa a Gasar Wasanni ta Afirka karo na 12 da ke gudana a kasar Maroko, a yau Juma’a da misalin karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya ne kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 20 ta Najeriya da aka fi sani da Flying Eagles za ta kece raini da takwararta ta Burkina Faso a wasan karshe na kwallon kafa na maza.

Rabon da Najeriya ta samu lambar zinare a kwallon kafa na maza a gasar wasanni ta Afirka tun a 1973 kimanin shekara 46 da suka gabata. Sai dai Najeriya ta samu lambar tagulla a gasar da aka yi a Kongo Brazzabille a shekarar 2015.

Najeriya ta kai wannan matsayi ne bayan ta lallasa Mali da ci 5-4 a bugun finareti kamar yadda Burkina Faso ta kai wannan matsayi bayan ta lallasa Senegal da ci 5-4 a bugun finareti.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun Ministan Matasa da Wasanni Mista Sunday Dare ya aike da sakon taya murna ga Flying Eagles inda ya bukaci su dage don gann sun lashe lambar zinare a wasan na yau don daukaka martabar kasar nan a Afirka da duniya baki daya.