✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martani daga makaranta (1)

Yau ma kamar kodayaushe na ba makaranta wannan shafi damar su tofa albarkacin bakinsu a kan wadansu batutuwa da muka tattauna a cikin watannin da…

Yau ma kamar kodayaushe na ba makaranta wannan shafi damar su tofa albarkacin bakinsu a kan wadansu batutuwa da muka tattauna a cikin watannin da suka shige. Da yake abin da yawa, na tsakuro ne daga daruruwan martanoni da aka yi mini. Da fatar wannan kafa ta kasance hanyar kara ilimantar da juna da karin fadakarwa, na gode!

Batun Wa ya tsine wa Najeriya?
Yasir Ramadan Gwale: Da kyar idan ba tsine wa Najeriya aka yi ba.
Bash Twins: Allah gafarta Malam, tabbas, wadannan amsoshi abin nema ne. Kazalika, tsinuwa da baki sun kama Najeriya, kuma da alama alhakin kananan ’ya’ya da jikokin ne, ya haifar wa uwar halin da take ciki a yanzu.
Bashir Lawal: Madallah da kai malami ma’abocin nazari….tabbas wasu ne ina ganin daga cikin manyan ’ya’yan Najeriya suka tsine wa Najeriya, kuma tsinuwar ta bi ta…haka nan ba tare da hakkinta ba…sai ga shi yanzu sun ja wa ’ya’yanta na baya… Kuma su ma sai da suka gama cin moriyarta sannan suka tsine mata don kada wasu su biyo bayansu su ma su amfana da uwarsu…wannan ya fito ne daga sawun:
Hassada  
kyashi
Ganin gari.
Hadama
Halin bera
Daga mu sai ’ya’ya da sauransu.
Wannan ya sa Najeriya ta zama marainiya sakamakon manyan ’ya’yanta na farko-farko wadanda suka bijire mata har ta kai su ga sa-in-sa…suka la’anci juna…. Amma ina ganin har yanzu za a iya nema musu gafara, a nemi yafiyar wannan tsinuwa ta Najeriya don a manta da komai a dawo a sulhunta tsakanin uwa da ’ya’yanta…sai ya zamana an koma ana morar juna komai ya daidaita ’ya’yanta na gari su zamana a kan gaba.
Adamu Ago Gsh: Ina ganin abin nan da ake cewa, ɗan kuka mai jawo wa uwarsa jifa ne. Domin kuwa, waɗanda suka haifi Najeriya wato magabatan farko, sun ɗora ta kan turba tagari. Amma kash! Ita kuwa sai ta hayayyafa da nagartattu da kuma latatattu. Waɗannan latatattun ’ya’ya nata su ne ke riƙe da ita a halin da ake ciki.
Ghazali Imam: A fahimtata tsinuwar ta wanzu ne saboda 1- Azzaluman shugabanni. 2- Dattawa ko tsofaffi masu kwadayi (domin idan akwai kwadayi ba za a iya fadin gaskiya ba). 3- Matasa marasa alkibla da sanin makoma. 4- Malamai da sarakuna da ’yan siyasa masu son kansu.
Abdul Ango: Alhakin jinin bayin Allah da aka zubar ne a yayin juyin mulkin sha biyar ga Janairu 1966 yake bin Najeriya, ma’ana jinin su Sardauna da Tafawa balewa, adalan shugabanni, bayin Allah na gaske, masu fada da cikawa. Sukurkucewar Najeriya ta samo asali ne daga wannan rana.
Abubakar Yusuf Shelleng: Duk abin da yake da farko yana da karshe, ai kullum cewa ake kada mu yanke kauna domin in na lura da bayaninka me ke faruwa, sannan mene ne mafita? A ra’ayina addu’a da kuma gyara halinmu da cire son zuciya da son kai da kabilanci da bambancin addini da rashin tsoron Allah su ne ginshikin magance tsinuwa da muke fama da ita. Mu tuna fa mulki na dawwama ko na kafirai ne in da adalci, amma muddin Musulmi zai mulki da rashin adalci sunansa fadadde, jama’arsa kuma wahallallu.
Umar Sidi Ahmed: Tsinuwar da Najeriya ke fama da ita abin har ya yi mata yawa, shugabanni suna tsine wa talakawa, talakawa suna tsinuwa ga shugabanni, malamai suna tsinuwa ga ’yan uwansu, jahilai suna tsinuwa ga malamai, mawadata suna tsinuwa ga mabukata, yayin da mabukata ke tsinuwa ga mawadata. Haka kuma manya suna tsinuwa ga kanana, alhali su kuma kanana suna tsinuwa ga manya.  dan Arewa ya tsine wa dan Kudu, shi ma dan Kudu ya tsine wa dan Arewa. Haka tsinuwar take tsakanin Musulmi da wanda ba Musulmi ba ko tsakanin Musulmi da Musulmi, irin wadannan ne suka tattara suka fada wa kasar, sai tsinuwar ta koma wa Najeriya ta inda kowa zai dandana.
Bala Abdullahi: Amsar wadannan tambayoyi ba abu ba ne mai wahala ba, domin idan mutum na iya tsine wa kansa kuma ya ga tasirin wannan tsinuwa a rayuwarsa, to ina ganin ba laifi aka yi ba idan aka ce NAJERIYA ita da kanta ta tsine wa kanta. Don haka mifita a gare ta shi ne ta yafe wa kanta, kuma mataki na farko na samun yafiya shi ne ta zabi yara nagari don gudanar da al’amuranta don a fara samun mafita.

Za mu ci gaba