Da Dumi Dumi

Martani ga Gwamna El-Rufa’i

Assalamu alaikum Edita. Furucin Gwamna El-Rufa’i cewa Najeriya kasa biyu ce Kudu da take jagaba da Arewa da ke ci-baya bai dace ba. Abin da ya sa na ce haka shi ne ai El-Rufa’i ne shugaban da Obasanjo ya nada wajen dakatar da dimbin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya a wa’adi na biyu na mulkin Obasanjo lamarin da ya shafi ma’aikata fiye da kashi 60 daga cikin 100 kuma cikin wadanda aka dakatar kashi 40 ko fiye da haka ’yan Arewa ne. Abin takaici shi ne ba a bi sharuddan da bangaren da aka bai wa nauyin zartar da hakan suka zayyana ba, domin son rai aka yi don kau da ’yan Arewa da za su iya zama wani abu a gaba. Kuma duniya su sani cewa bayan dakatar da mu da aka yi a lokacin bagatatan ba a fara biyanmu ba sai bayan shekara biyu lokacin ma dan Arewa ne Babban Akanta na Kasa, Alhaji Ibrahim Dankwambo, bayan Obasanjo ya ce za a biya hakkinmu. Haka ya rage sojoji da aka yi ai don kawar da dimbin sojoji ’yan Arewa ne da suke ji barazana ne a gare su.

Daga Muhammad Gombe, 08036191792.

 

Obasanjo ka iya bakinka

Salam Edita. Ka ba ni dama in yi tsokaci game da kalaman tashin hankali da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ke furtawa.  A gaskiya irin wadannan maganganu nasa za su iya kawo Yakin Basasa a kasar nan. Muna yi masa kallon dattijo mai yawan shekaru kuma wanda ya mulki kasar nan ba sau daya ba amma abin takaici da bakin ciki shi ne yadda yake sakin baki yana fadin wasu maganganu da ba su dace abin bai dace ba a ce kamarsa yana yin su ba. Obasanjo ka sani in ba ka kama bakinka ba, to duk abin da ya same ka, ka kuka da kanka.

ADVERTISEMENT

Daga Tukur Sani Kwasara, Karamar Hukumar Bagudo, Jihar Kebbi  08086408131

Fatan alheri ga ministocin Buhari

Salam Edita. Ka ba ni dama in taya daukacin ministocin Shugaba Buhari murnar rantsar da su da aka yi a shekaranjiya Laraba.  Ku tuna Allah ne Ya zabe ku ba don kun fi  saura cancanta ba.  Ku tuna mulki na Allah ne, Yana bayarwa ne ga wanda Ya so kuma lokacin da Ya so.  Yanzu ’yan Najeriya sun zuba ido su ga irin wainar da za ku toya.  Idan kuka yi mai kyau, ko shakka babu za ku ga mai kyau  haka idan kuka yi akasin haka, to alhaki na kanku ne.

Da fatan za ku share wa talakawa hawaye musamman a wannan lokaci da ake fama da kuncin rayuwa.

Daga Zainab Yusuf (Zee ’Yar mamanta)  08036475927

Yabo ga Gwamnan Jihar Zamfara

Assalam Edita. Don Allah ina so ka ba ni dama in yi tsokaci a kan ci gaban da Jihar Zamfara ta samu bayan nasarar da Jam’iyyar PDP ta samu a kotu.  Gaskiya yanzu talakawan Jihar Zamfara suna jin dadin yadda wannan gwamnati take tafiyar da mulkinta musamman a bangaren magance matsalar tsaro.  Da fatan Allah Ya ci gaba da kawo mana zaman lafiya a jiharmu da kasa baki daya.

Daga Anas Abdulkarim Liman Kurya Madara, Jihar Zamfara .  08060377275

Kira ga Hukumar NCC

Salam Editan Aminiya. Zan so ka ba ni dama in mika kukana ga Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya (NCC), cewa ta sani ba matsalar yin rajistar layuka ga ’yan Najeriya ce kadai matsala ba.  Wata babbar matsalar ita ce yadda kamfanonin sadarwa ke kwashe wa  abokan huldarsu kudi babu gaira babu dalili.

Alal misali Kamfanin MTN ya bullo da wata dabarar cutar mutane inda zai turo wani sako ya nemi mutum ya danna wata lamba a matsayin ya amince ko da sani ko ba da saninsa ba.  Mafi yawan wadanda suke hulda da kamfanin ba su da masaniya don haka da zarar sun latsa wannan lamba sai kawai a rika kwashe musu kudin da suka sanya a wayar tasu.

Ina ganin wannan wata hanya ce ta mayar da kudin da Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar NCC ta ci tarar kamfanin biliyoyin Naira a watannin baya.

Yana da kyau Hukumar NCC ta kafa kwamitin da zai binciki wannan badakalar kuma idan ta samu Kamfanin MTN da laifi to lallai ta sake cin tararsa.

Daga Mubarak Sagir Gama   08039151742

Wakilan Jihar Sakkwato ku ji tsoron Allah

Salam Edita. Da fatan an yi shagulgulan Sallah lafiya. Zan so ka ba ni dama in yi kira ga masu wakiltar Jihar Sakkwato a Majalisar Dokoki ta Kasa irin su Alhaji Musa Sarkin Adar mai wakiltar Gada da Goronyo da Sanatan Sakkwato ta Gabas su ji tsoron Allah su tuna akwai ranar da Allah zai tambaye su game da yadda suka wakilci al’ummar Sakkwato a majalisa. Da alama babu wani yunkuri da suke yi na ganin an kawo karshen hare-haren da ’yan bindiga suke yi a Jihar Sakkwato kamar yadda aka shawo kan al’amarin a Jihar Zamfara.

Daga mai lamba  08128028641

Kukanmu ga Shugaba Buhari

Salam Edita. Zan so in yi tsokaci a kan yadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai cika kula da yankin Arewa ba.  Alal misali yadda ake kai wa yankin Arewa musamman Arewa maso Yamma hare-hare ta hanyar kisan gilla da garkuwa da mutane don kudin fansa da yadda aka sace mana mata da ’ya’ya da kuma sace mana dabbobi abin sai addu’a.

Baba Buhari ya kamata ka kawo mana dauki cikin gaggawa don mu san kai danmu ne.

Daga Sanusi Haruna, 09069023896

Sakon Sallah ga ma’aikatan Aminiya

Edita ina taya daukacin ma’aikatan jaridar Aminiya murnar Sallar Layya.  Da fatan an yi shagulgulan Sallah lafiya.  A gaskiya Aminiya tana burge ni wajen zakulo mana sahihan labarai da kuma wayar mana da kai.  Muna jinjina muku, Allah Ya saka da alheri.

Murtala Ahmed Abubakar, Kwalli Gidan Doki 07068295953

Allah Ya dawo da Alhazanmu lafiya

Ina yi wa Shugaban Karamar Hukumar Soba da ’yan majalisarsa Barka da Sallah.  Da fatan alhazanmu sun gama aikin Hajji lafiya kuma za su dawo gida lafiya.

Daga Isah Murtala Gama-gira,  08135419744

Gobara ga ’yan kasuwar Funtuwa

Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!  Ina yi wa daukacin ’yan kasuwar da ke bakin Babban Asibitin Funtuwa jaje game da gobarar da ta tashi a kasuwar a kwanakin baya. Da fatan Allah Ya mayar musu da dukiya mafi alheri.  A gaskiya muna kira ga gwamnati ta kai musu dauki.

Daga Sa’adu Sani Baffa Funtuwa, Unguwar M/Makera  09092577473 ko 08067229431

Kira ga kotun zaben Kano

Ina kira ga Mai shari’a Halima Shamaki ta tsaya tsayin-daka tsakaninta da Allah ta yi adalci a hukuncin da za ta yanke a zaben da ya gudana a bana.  Mai gaskiya ta ba shi gaskiyarsa, sannan marar gaskiya ta ba shi rashin gaskiya.  Da fatan Allah Ya taimake ki.

Daga Al’ummar Yawale Jihar Kano  07060869537

Ta’aziyya ga Jami’ar ATBU Bauchi

Salam Edita. Ina so ka ba ni dama in mika ta’aziyya da jaje ga mahukunta Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) da ke Bauchi game da rasuwar wadansu dalibai bayan wata gada ta karye.  Wadanda suka rasu Allah Ya jikansu da rahama yayin da wadanda suka jikkata Allah Ya ba su lafiya.  Ga iyalan wadanda suka rasu kuma Allah Ya ba ku hakurin jure wannan rashi.

Daga Saminu Artillery Yelwa Shendam Jihar Filato 08032436477

A rika daukar ’yan sakandare aikin dan sanda

Salam Edita. Ina so ka mika kukana ga wadanda alhakin daukar ’yan sanda ya rataya a wuyansu. A gaskiya yadda ake yin biris da masu shaidar karatu ta sakandare wajen daukar aikin ’yan sanda a kasar nan abin bai dace ba. Domin da yawa daga cikin masu irin wannan shaidar karatu ba su da halin ci gaba da zurfafa iliminsu kuma ba su da wata sana’a ko wata hanyar samun kudi sai zaman kashe wando kawai.

A tawa fahimtar da za a rika taimaka musu wajen daukar aikin dan sanda hakan zai karfafa samar da tsaro a kasar nan don su ma suna da irin tasu gudunmawar da za su iya bayarwa a aikin dan sanda.

Daga B. Promise (Baban Iya),  08149601454.

Maraba da sake kama Wadume

Salam Edita. ina fata zan samu fili don in yi sharhi game da sake kama wanda ake zargin ya kare wajen yin garkuwa da mutane Hamisu Bala da aka fi sani da Wadume.  Mun yi bakin ciki a kwanakin baya da muka samu labarin ’yan sanda sun kama shi amma wadansu batagarin sojoji suka kashe su inda aka shiga yin bincike. Yanzu dai gaskiya ta bayyana bayan an sake kama wanda ake zargin, inda ya fallasa wadanda suka hada baki aka kubutar da shi. Don haka muna jinjina ga ’yan sandan da suka sake kamo shi don ya fuskanci hukunci.

Daga Jibril Abba Ocal, 08053932787

Zuwa ga Buhari 

Lallai ya tabbata ’yan arewa kawai kake mulka ’yan Kudu suna mulkarka. Ina zuciyarka ta jarumin soja da aka ce kana da ita? An ce kai kaifi daya ne in za ka yi abu ba wanda ya isa ya hana ka, amma sai ga shi kana tsoron ’yan Kudu.  Idan za ka yi shirinka na ruga da ka yi niyya ka yi. Allah Ya taimake ka Ya ba ka ikon aikata abin alherin da ka yi niyya.

Daga Hadi Imam Batsari 08108028015.

Share