✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Martanin mutuwa rigar kowa

Yau kuma mun ba masu karatu dama ne su amayar da abin da ke zuciyarsu game da abubuwan da muka tattauna a wannan shafi. Da…

Yau kuma mun ba masu karatu dama ne su amayar da abin da ke zuciyarsu game da abubuwan da muka tattauna a wannan shafi. Da fatar za a amfana kamar yadda aka saba.

Mun gode

Baida’u Gada

Wallahi abin da ke faruwa ke nan sai dai ba kowa zai gane ba sai wanda ya fada halin rashi, ni shaida ce domin hakan ya faru da mu lokacin da na yi rashin mijina bayan addu’ar uku ko ma in ce bakwai kofar gidanmu tsit kamar an yi ruwa an dauke. Duk irin dimbim jama’ar da mijina ke da su kasancewarsa mutumin mutane amma shiru muka ji ba mu ganin kowa sai kalilan daga cikinsu wadanda suka rike amana su ne har yanzu suke ba mu kula.

Zancen gaskiya ido ake yiwa ba kowa ke yi don Allah ba musamman yanzu da ba zumunci, kowa gidansa da iyalansa ya sani sai dai fatar Allah Ya ganar da su gaskiya Ya sa mu fi karfin zukatanmu.

Allah Ya kara wa Farfesa lafiya da rayuwa mai albarka.

Rabe Ahmed Yantuwaru

Wannan ita ce dabiar al’umarmu a wannan zamani. Shaukin awalaja ya sa ba mu iya yin komai a kan wani da ba namu ba .

Allah Ya kara mana aminci da kaunar juna.

Allah Ya kara wa rayuwa albarka.

Mubarak Idris Jikamshi

Da a ce duniya da mutanen cikinta za su tafi bisa wannan gwadaben (turba) da lallai maraici ya kare. Gaskiyar Bahaushe da yake cewa ‘Ba a maraya sai raggo.’ Idan kuwa, har za mu yi amfani da wannan nasiha, ni da kai, da ita, su da mu da ku, lallai za mu kawo canji mai dorewa, kuma marayu za su daina tagayyara, marasa karfi za su samu sukuni da kuzari gami da karsashi domin ganin an mutunta juna. Allah Ya sanya mu dace.

Safiyanu Sani Sani

Allah Ya saka wa Malam da alheri a kan wannan tunatarwa da aka yi mana. Allah Ka ba mu ikon gyara halayenmu da dabi’unmu. Malam Allah Ya saka maka da gidan Aljanna.

Muhammad Mahmud

Allah Ya kyauta. Wannan kam fadakarwa ce mai matukar muhimmanci. Allah Ya ba mu ikon gyarawa.

Hassana  Abdullahi Hunkuyi

Allah Ya kyauta, haka abin yake, ba a taimakon masu bukata sai sun yi hijira zuwa Lahira, wai sai a shiga nuna musu kauna.

    Maryma  Aliko  Mohammed

May we be reminded. Allah Ya iya mana, amin.

    Alamuna Nuhu

Allah Ya sa mu cika da imani. Wadanda suka riga mu Allah Ya gafarta musu, Ya kyautata karshensu. Allah Ya jikan Malam da rahama. Allah Ya raya abin da ya bari.

    Shamsu Hamza

Fatawata ga Malam ita ce: bambancin da ke tsakanin jimlolin ‘Tonon asiri’ da Tonon silili’ domin ni a nawa tunanin duk daya ne. Bambanta sun da ka yi shi ya ja hankalina.

    Sani Fari Abdu

Madubin rayuwa cikin kalamai masu nazartarwa da bijirar da hakikanin mai wanzuwa.

Allah Ya saka da alheri, Ya sanya mu gama da duniya lafiya da yanayi mai kyau a Lahira.

    Abdullahi Abdullahi  Jayawa

Allah Ya saka da alheri, Ya kuma jikan iyayenmu da kakanninmu. Allah Ya kara lafiya da basira Malam.

    Bilkisu Yusuf Ali

Allah Ya sa mu fadaka. Allah in mutuwa ta zo gare mu ta same mu muna farare tas alfarmar Shugaba Muhammad (SAW). Gatan adabi mun gode kwarai da fadakarwa.

    Rabi’u Bishir

Haka rayuwa take Farfesa, tabbas da Allah bai saka wa bawa mantuwa ba a kan mutuwa da ko ruwa ba zai iya hadiya ba. Fatan dukan Musulmi ya dace da rahamar Allah. Allah Ya gafarta mana baki daya Ya kuma sa mu cika da imani, shi kuma Farfesa ’Yandaki Allah Ya kai haske kabarinsa, Ya sa yana cikin Aljanna Madaukakiya. Ku kuma abokansa da ’yan uwa Allah Ya kara muku hakurin rashinsa.

    Rabi Mohammed

Allah Ya jikan wadanda suka riga mu, Ya jikanmu mu ma idan tamu ta kasance. Allah Ya ba da ladan tunatarwa Farfesa.

    H R Abubakar

Wannan kasidar ta kayatar, ta koyar tana kuma tsoratarwa. Allah Ya kara wa Malam hikima.

    Hajara Umar Jibril

Allah Ya sa mu cika da imani,  Ya sa mu dauki darussan da ke cikin wanann kasida amin.

    Adamu Lawal Mijinyawa

Ina ma dai Malam ya kammala da cewa ‘za mu ci gaba in Allah Ya yarda?! Ko ba yiwuwar mutuwa ta yi kutsen da Malam ke jan hankulanmu?

    Sirajo Ladan

Allahu Akbar! Jiya ba yau ba….Allah Ya jikan mamatanmu.

    Umar Alkasim Idris

Allah Ya jikanmu… Farfesa Allah Ya sa ladan a mizani.

    IB Sirajo

Allah Ya jikan magabatanmu, mu kuma Allah Ya sa mu cika da imani.