✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Marubucin littafin Hisnul Muslim ya rasu

Fitaccen Shehin Malamin addinin Musulunci nan, Sheikh Sa’eed bin Wahb Alkahdany wanda shi ne marubucin shahararren littafin addu’o’in nan, HISNUL MUSLIM, wanda aka fi sani…

Fitaccen Shehin Malamin addinin Musulunci nan, Sheikh Sa’eed bin Wahb Alkahdany wanda shi ne marubucin shahararren littafin addu’o’in nan, HISNUL MUSLIM, wanda aka fi sani da azkar a wasu kasashe, musamman Najeriya ya rasu.

Sheikh din ya rasu ne a ranar Litinin bayan Sallar Asuba, kamar yadda rahotanni suka nuna. Haka nan kuma an ruwaito cewa Shehin malamin ya rubuta sama da littattafai 80 a rayuwarsa, duk da cewa littafin Hisnul Muslim din ya fi sauran shahara, kuma da shi aka fi saninsa.

Tuni dai aka binne Shehin Malamin bayan an wa gawarsa Sallah a masallacin Arrajihy da ke garin Riyadh, Babban Birnin kasar Saudiya kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shi dai wannan littafin na Hisnul Muslim, wanda ke nufin Kariya Ga Musulmi, ya shahara a tsakanin Musulmin duniya wajen addu’o’in kariya daga sharrin mutum da aljan, domin ya tattara dukan addu’o’in da ake bukata domin gudanar da harkokin yau da kullum kamar yadda ke kunshe a hadisan Annabi (SAW).

Duk da cewa akwai littafan na addu’o’in neman kariya, amma littafin Hisnul Muslim ya yi zarra a tsakaninsu, wanda hakan ke nuni da tsarkin niyyar marubucin.