Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Maryam Booth ta yi murabusa daga Gidauniyar Atiku

Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Maryam Booth ta ajiye mukaminta na Mataimakiyar Shugaban Gudauniyar Atiku.

Maryam ta bayyana hakan a shafinta na Instagram mai suna @officialmaryambooth, inda ta ce, “ina so in yi amfani da wannan damar wajen bayyana cewa na ajiye mukamina na Mataimakiyar Shugaban Gidauniyar Atiku (Atiku Care Foundation) daga ranar 24 ga watan Disambar bana. Ina godiya bisa gudunmuwar da na samu a cikin watannin da na yi aiki da kuma damar da aka ba ni. Ba shakka na ji dadin lokacin da naked a gidauniyar. Ina godiya matuka.”

ADVERTISEMENT

Atiku Abubakar dai shi ne dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar PDP, kuma a kwanakin baya mun ruwaito yadda ’yan Kannuwood din suka rabu tsakanin Atiku Abubakar na PDP da Muhammadu Buhari na APC.

ADVERTISEMENT