Da Dumi Dumi

Masana sun yabi garambawul ga Kwamitin Tattalin Arzikin Kasa

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya  sauya Kwamitin Tattalin Arziki (EMT) da Mataimakinsa Yemi Osinbajo, yake jagoranta a ranar Litinin da ta gabata, inda ya maye gurbinsa da Majalisar Bayar da Shawara kan Tattalin Arziki (EAC) a karkashin jagorancin Farfesa Doyin Salami.

Lokacin da yake bayyana  kundin  kwamitin a ranar Litinin Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, ya ce majalisar za ta rika mika rahotonta ga Shugaban Kasa kai tsaye.

Mista Adesina, ya kara da cewa Shugaban Majalisar yana da ikon ganawa da Shugaban Kasa a kowane lokaci idan bukatar haka ta taso.

Mambobin majalisar sun hada da Dokta Muhammad Sagagi a matsayin Mataimakin Shugaba da Dokta Muhammad Adaya Salisu Babban Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Tsare-Tsaren Ci gaba a matsayin Sakatare da Farfesa Ode Ojowu da Dokta Shehu Yahaya da Dokta Iyabo Masha da Farfesa Chukwuma Soludo da kuma Mista Bismark Rewane.

Adesina ya ce majalisar za ta rika ba Shugaban Kasa shawara a kan tsare-tsaren tattalin arziki da harkokin kudade da ci gaban tattalin arziki wanda ya shafi harkokin tattalin arziki na cikin gida da kuma na duniya, kuma majalisar za ta yi aiki da shugabannin hukumomin hada-hadar kudade da sauran masu ruwa-da-tsaki a bangaren.

ADVERTISEMENT

Aminiya ta gano wannan shi ne karon farko da wani zai shugabanci irin wannan kwamiti ko majalisa ta tattalin arziki  daga wajen Fadar Shugaban Kasa.

Idan aka cire Mai ba Shugaban Kasa shawara ragowar ’yan majalisar ba sa cikin gwamnati.

Tsohon kwamitin da Mataimakin Shugaban Kasa ya shugabanta, mambobinsa duk suna da mukamai a gwamnati, sannan sun gana sau daya bayan rantsar da wannan gwamnati a karo na biyu.

Wadanda suka halarci ganawar daya tak da tsohon kwamitin ya yi a watan Agusta sun hada da  Ministan Kudi da Tsare-Tsare Hajiya Zainab Ahmad sai Ministan Masana’antu da Zuba Jari Mista Adeniyi Adebayo da Ministan Watsa Labarai da Al’adu Alhaji Lai Mohammed da Ministan Ayyuka Mista Raji Fashola da Minista a Ma’aikatar Kudi Clement Ike da Minista a Ma’aikatar Man fetur Mista Timpre Sylba.

Sai Gwamnan Babban Bankin Najeriya Mista Godwin Emefiele da Shugaban Kamfanin Man fetur na Kasa (NNPC), Alhaji Mele Kolo Kyari da Shugaban Hukumar Tara Kudaden Haraji ta Kasa (FIRS), Mista Babatunde Fowler da kuma wadansu daga cikin daraktocin hukumomin hada-hadar kudade na kasa.

Kamar yadda aka saba Maitaimakin Shugaban Kasa ne ke kula da Kwamitin Tattalin Arziki tun lokacin da aka dawo mulkin dimokuradiyya a 1999 .

Tsohon Shugaban Kasa  Cif Olusegun Obasanjo ya nada Mataimakinsa Atiku Abubakar a matsayin Shugaban Kwamitin Tattalin Arziki a tsawon zangon mulkinsa biyu.

Haka abin yake a lokacin mulkin Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa. Shi ma tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nada Mataimakinsa Namadi Sambo a matsayin Shugaban Kwamitin Tattalin Arziki na Kasa.

Wakilin Aminiya ya gano cewa  tun a shekarar 2015 ake sukar Shugaban Kasa kan sanya ministocinsa su mamaye kwamitin, sabanin abin da aka saba da shi a baya wajen hada ministoci da shugabannin manyan hukumomin hada-hadar kudade domin su hadu su rika ba  Shugaban Kasar shawara a kan harkar tattalin arziki.

 

Abin da masana tattalin arziki suka ce

Shugaban Kungiyar Masana Tattalin Arziki (EA), Dokta Ayo Teriba ya yaba wa Shugaban Kasa wajen nada wannan malajalisa da ya yi, ya ce hakan zai kara bunksa tattalin arzikin kasa.

Dokta Teriba ya taba shawartar Shugaba Buhari a kan ya kafa kwamitin tattalin arziki da zai rika ba shi shawara kai-tsaye tun lokacin da Shugaban ya cika kwana 100 a karagar mulki.Ya shaida wa wakilinmu ta tarho cewa abin a yaba wa Shugaban Kasa ne a kan wannan kokari da ya yi.

Wani masanin tattalin arziki da yake rike da wani babban mukami, wanda bai yarda a bayyana sunansa ba ya ce “Wannan babban ci gaba ne domin an dora kwarya a gurbinta domin an zabi masana wadanda suka goge a fannin tattalin arziki.”

Ya kara da cewa “tun farkon hawan wannan gwamnati mulki ta gaji mummunan yanayi na tattalin arziki  sannan ya sake  dada muni sakamakon rashin daukar mashawarta nagari da gwamnatin ta yi da farko. Abin takaici ne kwarai da gaske ganin yadda aka bata lokaci mai tsawo ba tare da kwalliya ta biya kudin sabuluba.”

Dokta Iorwuese Tyopeb, wanda masanin tattalin arziki ne da ke da kamfanin bayar da shawara da tuntuba a kan harkar kudade da ke Abuja ya ce “Daga nadin da Shugaban Kasa ya yi, za ka gane cewa an daura dan ba na ci gaban tattalin arziki. Shugaban Kasa ya nuna cewa lokacin da za a rika faranta wa ’yan siyasa ya wuce.”

Dakta Tyope ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaban Kasa zai yi amfani da shawarar da wannan kwamiti zai ba shi.

Ya ce “Na tabbata Shugaban Kasa zai yi aiki da shawarwarin da kwamitin zai ba shi. Ba ni da kokwanto a kan haka. Misali ya tarar da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya gada daga tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan kuma ya ci gaba da tafiya da shi ba tare da ya canja shi ba, sannan ya kara masa wani sabon zango,” inji shi

Tyope ya ce tunda dai ba wanda ya tilasta wa Shugaban Kasa  wajen kafa wannan kwamiti. To ba makawa yana da matukar sha’awar ci gaban tattalin arzikin kasa kuma tabbas zai yi aiki da shawarwarin wannan kwamiti.

 

 

Share