✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Jahun na da alaka da masarautar Kano – Hakimin Jahun

Ranka ya dade ko za ka fada mana tarihinka a takaice? Sunana Alhaji Balarabe Ahmed, Hakimin Jahun. An haifeni a 1962, yau ina da shekara…

Ranka ya dade ko za ka fada mana tarihinka a takaice?

Sunana Alhaji Balarabe Ahmed, Hakimin Jahun. An haifeni a 1962, yau ina da shekara 58 a duniya. Na yi firamare a Jahun kuma na yi Sakandire a Ungogo da ke Jihar Kano sai kuma na yi kwasa-kwasai daban-daban, kuma na yi aiki da Hukumar Aikin Gona ta Jihar Kano (KASCO), sannan na zama Hakimi a 1993 kuma ina da ’ya’ya 18 da mata biyu a halin yanzu. 

Daga wane lokaci ne Jahun ta fara mulki a matakin dagatai kuma dagatai nawa ta yi?

Dagacin Jahun na farko shi ne Sarki Jahuno wanda ya yi mulki a 1800 kuma ya yi shekara 30 yana mulki. Daga shi sai Sarki Leko wanda ya yi mulki daga 1830 zuwa 1835 sai kuma Sarki Kambari ya yi mulki a 1835 zuwa 1865 sai Sarki Also wanda ya yi mulki daga 1865 zuwa 1867sai Modibo daga 1867 zuwa 1883.  Sauran sun hada da Sarki Amadu a 1896 yayin da Sarki Shu’aibu ya yi mulki daga 1883 zuwa1897 daga shi sai Sarki Akilu daga 1908 zuwa 1945 sai Sarki Abubakar daga Abubakar Mai-mota har zuwa kan mahaifin Hakimi na yanzu wato Sarki Amadu dan Sarki ne, kuma jikan Sarki. 

Kafin a samu Jihar Jigawa, Jahun Sarki daya gare ta amma daga bayan aka raba masarautar Jahun zuwa gunduma biyar kuma aka raba Jahun zuwa dagatai uku, wato Sarkin Jahun Abudulahi da Sarki Abdullahi Musa da Sarki Haruna, wadannan gidaje uku ne suke jagoranta garin Jahun 

Yaushe Jahun ta koma tsarin hakimci?

An fara sarautar hakimci ne tun zamanin Turawan mulkin mallaka a 1906 kuma ta fara da Hakimi Abdullahi na Gwangwazo wanda ya yi sarauta daga 1906 zuwa 1925. Sai Abdu Barde wanda ya yi zamani daga 1925 zuwa 1945 daga shi sai Isma’ila Barde wanda ya yi zamani daga 1953 zuwa 1959 daga shi sai dan Amar Yakubu a 1961. Daga shi sai kuma Daban Kwano wanda ya yi zamani a 1964 zuwa 1970 sai dan Lawan Bashir wanda ya yi zamani daga 1976 zuwa 1976, sai Turaki Maje ya amsa daga 1966 zuwa 1974. 

Sauran sun hada da Sarkin Dawaki Mai Tuta da Baura da dan Makwayo da Magajin Rafin Dutse wanda shi ne Hakimin yanzu wato Alhaji Balarabe Ahmed daga shi sai Abubakar Bello Matawallen Dutse, sai kuma Alhaji Balarabe Ahmed bayan an kai shi Aujara ya yi wani dan zama aka sake dawo da shi Jahun din. 

Mene ne cikakken tarihin masarautar Jahun?

Masarautar Jahun tana da dogon tarihi. Tana da alaka mai yawa da wasu masarautu da ke Arewacin Najeriya, wata ta auratayya wata kuma ta yaki. Cikin wadanda ta yaka akwai Hadeja da Takalafiya da Zareku, sannan har yanzu saboda karfin sarautar Jahun akwai tambarin masarautar Hadeja yana nan a Jahun. 

Jahun mayaka ne sosai, wannan yana daya daga cikin abin da ya sa fadar Kano take alfahari da karamar Hukumar Jahun domin a zamanin ma ana cewa Sarkin Jahun Sarkin Gabas, ma’ana shi ne yake kula da Gabas da Kano. 

Ta fuskar auratayya ’yar Sarkin Jahun Akilu na wancan zamanin wanda ya yi mulki zamanin Turawan mulki mallaka ta yi aure ga marigayi Sarkin Kano Sunusi wadda ake ce wa Hajiya Gaji Mai Fulani wadda yanzu ’ya’yanta ne suke Sarautar Kano wadansu kuma hakimai ne a Jihar Kano. 

Ko Jahun na da kirari kamar yadda saurarn suke da shi?

Jahun tana da kirari kamar sauran garuruwa, ana yi wa Jahun kirari da ‘Jahuno Godi garin ’yar Sarki, idan da naka in babu naka ka shafa.” Jahun gari ne na Fulani makiyaya da suke da kwazo wajen noma da jarumta wajen yaki, mutane ne da ba su amince da raini ba. 

Da Jahun da Takalafiya da Hadeja da Miga sun taba zama karkashin ikon masarautar Jahun tun tana karkashin kulawar Sarkin Kano, kuma a wancan lokacin ita ce take amsar jangali da haraji tun daga nan Jahun har zuwa Sakkwato daga Jahun har zuwa Bauchi duk karkashin kulawar Mai Gabas ce wato Hakimin Jahun inda duk wani mai jajayen shanu yake biya.

Yaya alakar Sarki da talaka kafin zuwan siyasa?

Akwai dangantaka tsakanin sarakuna ta adalci. Su talakawa suna biyayya ga sarakuna kuma maganar cewar tsoron haraji ne ya sa talakawa suke yi wa masu mulki biyayya ba gaskiya ba ce, domin a zamanin ’yan siyasa na wancan zamanin sun yi kokarin lalata alakar, amma hakan bai yiwu ba saboda talakawan suna da kishin masarautun a wancan zamanin. 

Kuma maganar wai akwai rashin fahimta tsakanin ’yan siyasa da sarakuna babu ita, domin sarakuna ne suke taimakawa masu mulki. Ka dauki batun allurar foliyo, da babu sarakuna a ciki, mahukunta za su sha bakar wahala kafin su samu ikon shawo kan talakawa. Da sarakuna aka yi amfani wajen fadakar da al’umma muhimmancin allurar foliyo.

Da sojoji da ’yan siyasa su wa suka fi taimaka wa sarakuna?

Ai dukansu masu mulki ne kuma dukansu shugabanni ne kuma a gaskiya babu wadanda suka yi mulki babu tallafin sarakuna domin su sarakuna wata lema ce wadda dukan mai mulki yana amfani da su domin cimma wata bukata da kuma raya kasa.

Soke haraji da jangali bai taba martabar masarautu ba?

Ai bai taba darajar masarautu ba domin duk abin da hukuma take yi tana yi ne domin talakawa kuma su ne suke amfana. Duk da cewa ana cewa soke haraji da jangali ya sa an samu yawaitar kaurace kaurace daga wasu sassa zuwa wasu sassa na Najeriya, misali akwai Jahun a garin Bauchi, ainihinsu mutannen wannan Jahun din ne kuma mafiya yawansu sun tashi ne daga nan saboda yaki wadansu kuma sun yi gudun haraji ne.

Ka ce an samu ci gaba a zamanin Hakimin Jahun Turaki Maje me ya kawo?

A zamaninsa ne a 1966 aka kawo ruwan famfo kuma a 1970 aka mayar da Jahun zuwa karamar Hukuma, kuma a wannan lokacin ne karamar Hukumar Jahun ta samu wutar lantarki kuma Turaki Maje ne mutumin da ya yi fama da ’yan fashi irin su Maguza dan fashi da makami, wanda kowa ya san shi ne shugaban ’yan gunda kuma kowa ya san ’yan gunda barayi ne domin da tsakar rana suke bin kasuwa su je rumfar mutum su yi sata.Ba don Turaki Maje ba, da yadda ’yan gunda suka addabi jama’a a yankin Jahun da sauran masarautu da an sha bakar wahala. 

Shin me nene ma’anar ’yan gunda?

Gunda wani gungu ne na Fulani barayi da suke tare hanyar kasuwa suke wa ’yan kasuwa fashi ko su yi kwace a kasuwa ko kuma su yi amfani da kibiya su rika kan mai uwa da wabi su fasa taron jama’a su yi wa mutane sata ko a kasuwa ko a gidan biki ko a wani taro. Wato wata hada-ka ce ta barayi kuma duk wanda aka alakanta da gunda barawo ne. 

Akwai wani makadin Turaki Maje mai suna Ali Soso, shin gaskiya ne ya taimaka wajen bunkasar Jahun?

Gaskiya ne, Allah Ya jikan Ali Soso Ya jikan Turaki Maje. Allah Ya kai rahama gare su. Gaskiya Ali Soso ba karamar rawa ya taka ba wajen ci gaban Jahun domin ya yi amfani da damarsa ta waka wajen aika wa al’umma sakon fadakarwa.

Ko ita ma Jahun tana da ganuwa kamar sauran garuruwan?

Jahun tana da ganuwa kamar yadda sauran masarautu suke, kuma girman gari ne ya sa aka samu rushewar ganuwar kuma garin ya habaka matuka fiye da inda Jahun take a da.