Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Masarautar Kano za ta nada Naziru Ahmad Sarautar Sarkin Mawaka

Fadar Mai Martaba Sarkin Kano, ta sanar da nada shahararen mawakin Kannywood Nazir Ahmad a matsayin Sarkin Mawakan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi Na biyu.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan Fadar Kanon Alhaji Munir Sunusi, tace lura da gudummowar daya baiwa Sarkin Kano tun yana matsayin Dan Majen Kano, da kuma zamowarsa Sarki, yasa fadar ta girmama shi da wannan sarauta ta Sarkin mawaka.

ADVERTISEMENT

An tsaida ranar 27 ga watan Disamba 2018 a matsayin ranar da za’ayi bikin nadin sarautar a fadar Masarautar Kano.

ADVERTISEMENT