✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Sasa ta nada sabbin sarautu

Majalisar masarautar Sasa a Ibadan ta ce, nan ba da dadewa ba za ta sauke mutane 10 daga matsayin sarautun da masarautar ta nada su…

Majalisar masarautar Sasa a Ibadan ta ce, nan ba da dadewa ba za ta sauke mutane 10 daga matsayin sarautun da masarautar ta nada su domin maye gurbinsu da wasu mutane daban. 

Bayanin haka ya fito ne daga bakin Sardaunan Yamma Sarkin Sasa Alhaji Haruna Maiyasin cikin jawabinsa a lokacin da yake mika takardar shaida (certificate) ga Sarakunan Hausawa 3 daga Jihar Legas da Sarkin Yakin Yamma da aka daukaka matsayinsu zuwa masu rike da sarautu a jihohi 6 na yammacin kasa kuma ‘yan majalisar masarautar Sasa.

Sarakunan da suka karbi takardar shaidar a wajen bikin da aka yi a ranar lahadi a fadar Sarkin Sasa da ke Ibadan sun hada da Sarkin Hausawan Agege Alhaji Musa Muhammed Dogon Kadai da ya samu karin girma zuwa mataimakin Sardaunan Yamma da Sarkin Hausawan Ikotu Alhaji Nuhu Alhassan wanda aka daukaka matsayinsa zuwa Sarkin Bain a jihohin Yamma da Sarkin Hausawan Idi-Araba Alhaji Hassan Auyo da ya zama Garkuwan Yamma. Shi kuwa Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan ya samu takardar shaidar tabbatar masa da sarautar Sarkin Yakin Yamma ne.

Wasu muhimman dalilai sun hana Sarakunan Hausawan Agege da Idi-Araba zuwa karbar wannan shaida da aka mika wa wakilansu. Shi kuwa sabon Sarkin Yakin jihohin Yamma Alhaji Isma’ila Maikankan da sabon Sarkin Bai na jihohin Yamma, Sarkin Hausawan Ikotun Alhaji Nuhu Alhassan sun isa fadar Sarkin Sasa tare da dimbin jama’a ne domin karbar takardar shaidar da hannunsu.

Cikin jawabin sa Sarkin Sasa ya ce “daga yanzu dukkan wadannan shugabanni sun zama ‘yan majalisar masarautar Sasa da za a rinka tattauna batutuwan da suka shafi hadin kan jama’ar su da ci gaban su.”

Kuma ya nemi wadannan shugabanni da su yi amfani da matsayin na su wajen samo hanyar taimakawa mahukunta a kan ayyukan tsaron lafiyar al’umma a wannan sashe da kasa baki daya. Haka kuma ya nemi dukkan masu rike da sarautu su yi koyi da irin halayen Galadiman Yamma Alhaji Umar Adam da ya tashi tsaye wajen girmama fadar Sasa da fafutukar lalubo hanyoyin hadin kan jama’a da ci gaban su.

Da yake magana a madadin sauran sarakunan da suka samu karin girma, sabon Sarkin Yakin Yamma Alhaji Isma’ila Salihu Maikankan ya fara da rokon Allah (SWT) ne da ya yi masu jagoranci, inda ya ce, “Idan Allah Ya yarda daga yanzu za a fara ganin canjin al’amura da suka shafi hakkin ’yan Arewa a wannan sashe.”

Alhaji Ibrahim Plateau dan uwan Sarkin Yaki ne ya ce, “ina ganin na fi shi yin farin ciki a game da wannan matsayi da aka nada shin a jagorancin jama’a. Ina so ya yi amfani da wannan matsayi wajen janyo makiyansa a kusa da shi kuma ya rike jama’a da hannu biyu.”

Shi kuwa Malam Zakari Yusuf cewa ya yi, “ina godiya ga Allah (SWT) da Ya kawo mu wannan rana ta farin ciki. Shawarar da zan ba shi ita ce, ya yi kokarin hada kan jama’ar Agege da Jihar Legas baki daya.”