✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masarautar Waja ta nada Finney Dabid Jakadiyar Waja

Mai martaba Sarkin Waja (Bala Waja) Alhaji Muhammed Danjuma Muhammed ya nada Misis Finney Dabid, a sarautar Jakadiyar Waja ta farko. Finney Dabid, ’yar siyasa…

Mai martaba Sarkin Waja (Bala Waja) Alhaji Muhammed Danjuma Muhammed ya nada Misis Finney Dabid, a sarautar Jakadiyar Waja ta farko.

Finney Dabid, ’yar siyasa ce da ta yi takarar Majalisar Wakilai a karkashin Jam’iyyar APC amma ba ta yi nasara ba.

Mamba ce, a Hukumar Gudanarwar Hukumar Kula da Kayayyakin Tarihi ta Kasa. Har ila yau mamba ce a Hukumar Gudanarwar Kwalejin Kula da Lafiyar Dabbobi ta Tarayya da ke Ibadan.

Da yake bayyana dalilan nada ta sarautar Jakadiya, Bala Waja, Alhaji Muhammed Danjuma Muhammed, ya ce Finney ta taka rawar gani ne sosai wajen ci gaban Masarautar Waja, kuma nadin nata zai kara mata kwarin gwiwa.

Bala Waja, ya kara da cewa Masarautar Waja ta bai wa kimanin mata 50  sarautun gargajiya amma cikinsu ba wadda ta yi bikin wankan sarauta sai Finney wada ba a wuce wata uku da ba ta ba sarautar ba.

Basaraken ya yi mata addu’ar alheri na Allah Ya taya ta riko ta kuma samu karfin gwiwar ciyar da Masarautar Waja da Jihar Gombe gaba.

Da take jawabin godiya Misis Finney Dabid, ta gode wa Mai martaba Sarkin ne bisa wannan nadi da ya yi mata a matsayin Jakadiya ta Farko a tarihin kasar Waja inda ta ce, hakan zai kara jawo ta kusa da jama’ar masarautar.

Ta ce, za ta ci gaba da ba da gudunmawarta wajen samar wa matan yankin abubuwan dogaro da kai kasancewarta Shugabar Kungiyar Ci gaban Matan  Tangale Waja, Tangale Waja Debelopment Association (TAWADA).

Daga nan sai ta yi amfani da wannan damar ta kara gode wa matan kungiyarsu ta TAWADA bisa hadin kai da goyon baya da suke ba ta har ta kai ga matsayin da ta kai na Jakadiya.

Bayan kammala nadin nata an dora ta bisa doki ta zaga cikin garin Talasse  hedkwatar Karamar Hukumar Balanga a Jihar Gombe.