✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mashayin mai gadi ya bude wa Musulmi wuta a Osun

An samu hatsaniya da barazana ga rayuwar al’ummar Unguwar Aleluya Estate da ke garin Osogbo, Jihar Osun a shekaranjiya Laraba, yayin da wani maigadi da…

An samu hatsaniya da barazana ga rayuwar al’ummar Unguwar Aleluya Estate da ke garin Osogbo, Jihar Osun a shekaranjiya Laraba, yayin da wani maigadi da ya bugu da giya ya bude wa wadansu Musulmi wuta, lokacin da suke tafiya masallaci domin yin Sallar Asuba.

Daya daga cikin wadanda al’amarin ya rutsa da su, Alhaji Lukman Olaniyi ya ce suna cikin tafiya zuwa masallaci da misalin karfe 5:40 na asuba, sai suka ji karar harbin bindiga da yawa. Ya ce ashe wani maigadi ne yake biye da su a baya.

Haka shi ma Abdulwahid da al’amarin ya shafe shi, ya ce: “Mutumin ya yi nufin ya kashe mu ne. Muna hanyarmu ta tafiya masallaci sai muka ga ya fuskance mu da bindiga, sai ya fara harbin kan mai uwa da wabi. Mu kuma sai muka fara gudu domin tsira amma ya ci gaba da bin bayanmu. Allah ne kawai Ya cece mu, amma da ya hallaka mu.”

Wakilinmu ya tuntubi Rundunar ’Yan sandan Jihar, inda ta tabbatar da cewa ta riga ta kama mutumin da ake zargi da aikata harbin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Osun, Folasade Odoro ta ce bincikensu ya gano cewa mutumin wani maigadi ne da ya bugu da giya.

Shugaban Al’ummar Musulmin Jihar Osun, Alhaji Mustapha Olawuyi ya bayyana al’amarin a matsayin abin takaici. Ya yi kira ga hukumomin tsaro da sauran al’umma cewa lallai a kiyayi abin da zai jawo fitina a cikin al’umma, don haka a kiyayi abin da ya yi kama da tsokana ga al’ummar Musulmi a jihar.