Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Masoyin Buhari ya yi tattaki daga Abuja zuwa Kebbi

Wani masoyin Shugaba Buhari mai suna Sani Ahmed wanda a kwanakin baya ya fara tattaki daga Abuja zuwa Birnin Kebbi na Jihar Kebbi ya isa Birnin Kebbi.

Sani Ahmad ya samu tarbar matarsa, Sa’adatu da ’yarsa Aisha da sauran magoya bayan Jam’iyyar APC a filin wasa na Haliru Abdu da ke Birnin Kebbi, inda Sani ya ce daga nan zai wuce gidan gwamnati ne domin ya isar da sakon taya murna ga Gwamna Abubakar Atiku Bagudu bisa sake zabensa da aka yi.

ADVERTISEMENT

A cewar Sani, “Ma sha Allah. Yanzu na isa Birnin Kebbi, inda daga nan zan wuce Gidan Gwamnati.

ADVERTISEMENT