✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu adawa da karin kudin mai a Sudan sun kona ofisoshin gwamnati

Masu adawa da karin kudin mai a Sudan sun kona ofisoshin gwamnati, tare da ofisoshin jam’iyya mai mulki ta NCP da ke biranen Khartoum da…

Masu adawa da karin kudin mai a Sudan sun kona ofisoshin gwamnati, tare da ofisoshin jam’iyya mai mulki ta NCP da ke biranen Khartoum da Omdurman. Mutum biyu ne suka rasa rayukansu a zanga-zangar adawa da janye tallafin man fetur a kasar Sudan, kamar yadda jami’an ’yan sanda da iyalan mamatan suka tabbatar wa manema labarai.
An fara wannan zanga-zangar ne tun a ranar Talata, inda aka al’amarin ya zama tarzoma a ranar Laraba, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaraina AFP.
A ranar Litinin din d ata gabat ne gwamnati a bayar da sanarwar karin farashin albarkatun man fetur, bayan a janye tallafin da take bayarwa, don gyaran tattlin arzikin kasa.
Wadanda al’amarin ya auku a gaban idonsu, sun bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. “Masu zanga-zangar sun wawushe ofisoshin gwamnati, sun cinna musu wuta, har da ofishin Jam’iyyar NCP da ke Khartoum da kuma na birnin Omdurman.
Tuni dai tsadar rayuwa ta karu da kashi 40 cikin 100 a kasar Sudan. Shugaba Omar Al Bashir, ya bayyana a ranar Lahadin makon jiya, cewa “biyan tallafi na tattare da hadarin rusa tattalin arziki.”