Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Masu fasa bututun man fetur sun shiga komar ‘yan sanda

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wasu mutum biyar da ake zargi da fasa bututun mai a yankin Magboro da ke Ibafo a jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar DSP Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Aminiya cewa, jami’an rundunar sun kame wadanda ake zargin , a lokacin da DPO  ‘yan sandan ‘yankin SP Abiodun, ke aikin sintiri tare da wasu daga cikin jami’an ‘yan sandan yankin.

ADVERTISEMENT

”Sun yi kicibis da wadanda ake zargin suna kwasar  man fetur daga wani bututun mai da suka fasa, an kama su da jarkokin dibar mai lita 50 guda 12  cike da man fetur, a lokacin da suka ga jami’an mu sai suka ruga a guje suka ranta a na kare, nan take jami’an suka far masu suka kame su”. In ji shi.

 

ADVERTISEMENT