✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu fataucin ganda mai guba sun shiga hannu a Legas

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta yi kama wadansu mutum shida da ake zargi da hada-hadar ganda mai guba. Mai magana da yawun Rundunar ’Yan…

Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas ta yi kama wadansu mutum shida da ake zargi da hada-hadar ganda mai guba.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Bala Elkana ya shaida wa Aminiya cewa da sanyin safiyar Lahadin da ta gabata ce jami’an rundunar suka samu bayanan sirri game da mutanen da suke fataucin gandar mai guba, “Jami’anmu sun yi wa wadanda ake zargin dirar mikiya a yankin Igando da misalin karfe 5 na safe inda suka same su da tarin fatar shanu mai guba wacce aka jibge ta a wata rumfa ana kokarin rarrabata a kasuwanin yankin,” inji shi.

Ya ce, rundunar ta kama tarin gandar mai guba da motar da aka yiwo safararta tare da sinadari mai guba da ake zuba mata don hana ta lalacewa, an kuma kama mutum shida da ake zargi, wadanda suka hada da, Adelowo Yinka da  Olawumi Onabanjo da  Omowumi Wasiu da Adesokan Taiwo da Iyabo Oluwa da kuma Taye Kazeem. “Mun tuntubi jami’an kiwon lafiya na Jihar Legas wadanda suka yi gwaji a kan gandar suka kuma tabbatar tana dauke da guba wacce za ta yi lahani ga wanda ya ci gandar. Yanzu haka ana ci gaba da bincike domin gano wurin da aka shigo da gandar za kuma a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar mun kammala bincike,” inji shi.

Al’umar yankin Kurmi na yawan amfani da ganda wacce aka fi sani da komo a abincinsu inda sau tari sukan fi ba ta fifiko fiye da nama lamarin da ya sanya batagari ke fataucin gandar ta kowane hali.