✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa 16 sun shiga komar ‘yan sanda a Kano bayan kubutar da wasu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi nasarar kubutar da mutum biyu daga hannun masu garkuwa da mutane ta kuma kame mutum 16 da ake zargi…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi nasarar kubutar da mutum biyu daga hannun masu garkuwa da mutane ta kuma kame mutum 16 da ake zargi da kasancewa ‘yan garkuwa da mutane ne, ciki harda matar nan da ake zargi da garkuwa da yarinya wacce ta jefa a rijiya bayan ta nemi iyayenta su bada kudin fansa, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar yarinyar.

Wasu daga cikin makaman da ‘yan sandan suka kama

Haka zalika rundunar ‘yan sandan Kano ta kame ‘yan fashi da makami 9 da ‘yan daba 34 da karin mutum 54 da ake zargi da laifuka daban-daban, bugu da kari ta kame wasu ‘yan danfarar da ke hada-hadar filaye inda aka same su da kudi Naira dubu 400 da motoci 4 da kuma kame wani mutum a maboyarsa a garin Warawa wanda ake zargi da kashe wani mutum, kana ta kame tarin makamai da babur da kakin sojin da sauran su, wadanda da aka bajewa manema labarai a jiya Juma’a domin su shaida da idanun su.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Ahmad Iliyasu wanda ya jagorancin baje kolin wadanda ake zargin shaidawa Aminiya cewa, ko kadan rundunar ba zata saurarawa a jihar ba, ya ce tsarin nan na kawar da batagari da miyagu da babban sufeton rundunar ya kaddamar a fadin kasar nan na cimma nasar a jihar Kano.