Aminiya

Masu garkuwa da dalibai mata a Kaduna sun bukaci a biya Naira Miliyan 10

Masu garkuwa da mutane da suka sace dalibai mata shida da malamai biyu a Kwalejin Engraver, a  Kakau Daji, Karamar Hukumar Chikun jihar Kaduna. Suna ci gaba da tattaunawa da iyayen daliban makarantar don bin hanyar da za a sako daliban.

Masu garkuwan a yanzu sun bukaci a biya Naira Miliyan 10 ga duk kowa ce daliba da iyalan malaman biyu da aka yi garkuwan da su.

An dai yi garkuwan da daliban ne a ranar Alhamis ta makon jiya a harabar makarantar. Da farko dai masu garkuwan sun bukaci a biya kudin fansa Naira Miliyan 50 na duk dalibai shida da malaman makarantar.