✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mu ba su yi mana fyade ba mun sha azaba – ‘Yan mata 

Wasu ‘yan mata ‘yan garin Offa da ke jihar Kwara da aka yi garkuwa da su sun bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwa da su…

Wasu ‘yan mata ‘yan garin Offa da ke jihar Kwara da aka yi garkuwa da su sun bayyana cewa, wadanda suka yi garkuwa da su basu yi masu fyade ba, amma sun azabtar da su a kwanaki ukun da suka yi a hannunsu.

‘Yan matan tare da wasu maza uku da wata yarinya ‘yar karama an sace su ne akan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadin da ta gabata.

Sojoin Najeriya ne suka yi nasarar ceto su daga cikin dajin Rijana a wani samame da suka kai sansanin masu garkuwa da mutanen da safiyar jiya Laraba.

Aishat Aliyu Bisola, daya ce daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su ta kuma ce wadanda suka yi garkuwa da su Fulani ne kuma suna sanye ne da kayan sojoji a daren da suka tare su akan hanyarsu ta zuwa Kaduna.

“Da suka tare mu suna sanye ne da kayan sojoji daga nan suka wuce da mu cikin daji sai da muka yi tafiyar sa’oi uku cikin daji kafin muka kai sansaninsu da ke akan wani tsauni. Anan suka ajiyemu suka ce sai an biyasu Naira miliyan goma kafin su sake mu.

“Da gari yawaye watau ranar Litinin sai suka rage kudin zuwa Naira miliyan biyar. A Ranar Talata bayan sun lura iyayenmu ba su da wannan kudi sai suka ce, toh a kawo Naira miliyan biyu. Basu yi mana fyade ba amma dai sun rika dukanmu da kuma azabtar da mu ta hanyar hana mu abinci da ruwan sha.” In ji ta.

Haka itama Kadija Kehinde Okunola, ta ce babu wacce aka yi wa fyade a cikinsu sai dai kurum sun sha duka.

“Abin da kawai suke mana shi ne duka tare da matsa mana cewa akawo masu kudi. Domin su wai kudi kurum suke so. Amma basu yi mana fyade ba. Kuma basu buge karamar kanwata da ke tare da mu a cikin dajin ba.” In ji ta.

‘Yan Matan sun kuma bayyanawa Aminiya cewa, a lok‎acin da sojojin suka isa dajin suka fara harbi sai yan ta’addan suka gudu cikin daji suka bar makamansu da harsasai domin kada a kama su.

An dai mika su bakwai da aka ceto zuwa ga gwamnati jihar Kaduna wanda tasa a kaisu asibiti domin duba lafiyarsu kafin a mika su ga shugabanin Kungiyar Offa mazauna jihar Kaduna.