✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun aiko min da wasikar barazana – Dan majalisa

Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Shehu Yunusa Pambeguwa ya bayyana yadda masu satar mutane suka aike masa da wasikar barazana. Ya…

Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Shehu Yunusa Pambeguwa ya bayyana yadda masu satar mutane suka aike masa da wasikar barazana.

Ya bayyana haka ne lokacin da Kwamishinan Harkokin Cikin Gida, Samuel Aruwan ya bayyana a gaban majalisar domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa a ranar Litinin.

Dan majalisa Shehu Yunusa ya kara da cewa babu isasshen tsaro a majalisar haka kuma a gidajensu wanda hakan ke bai wa ’yan bangar siyasa damar zuwa ofishohinsu suna yi musu barazana.

“Babu tsaro a wannan majalisa domin ko a lokacin tantance mu da aka yi sai da ’yan bangar siyasa suka shigo har cikin ofisoshinmu. Saboda haka babu issassun jami’an tsaro a majalisar nan da gidajenmu,” inji shi

Dan majalisar ya bada misalin yadda aka sace daya daga cikinsu a watannin baya, “Duk da cewa a kan hanya aka sace shi amma ko a gidaje, muna samun barazana. Akwai lokacin da sai da na bukaci a ba ni ’yan sanda domin su rika kare gidana inda iyalaina suke saboda masu garkuwa da mutane sun aiko min da wasika da saurans,” inji shi.

A jawabin Mista Samuel Aruwan ya roki ’yan majalisar su taimaka su sa masa wani lokaci da zai zo su gana domin ya bayyana musu kokarin da gwamnati ke yi domin magance matsalar tsaro a jihar domin akwai bayanan da ba zai iya fadi a gaban ’yan jarida ba.