✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun hana mu sakat – Mutanen Igabi

Wadansu mutane wadanda akasarinsu manoma ne a Karamar Hukumar Igabi sun ce masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa sun tilasta musu kaurace wa…

Wadansu mutane wadanda akasarinsu manoma ne a Karamar Hukumar Igabi sun ce masu garkuwa da mutane domin amsar kudin fansa sun tilasta musu kaurace wa gonakinsu saboda tsoro.

Wadansu daga cikin manoman da suka tattauna da Aminiya, sun ce duk da cewa sun yi noma a bana amma dole ta sanya sun kaurace wa gonakinsu, sun kasa zuwa su girbe amfanin da suka samu. Sun yi zargin cewa ’yan bindiga da suke zaton Fulani ne suke tsare hanyar zuwa gonakinsu, wacce ke da nisan kilomita uku daga tashar jirgin kasa da ke Rigasa.

Wani manomi da ya bayyana sunansa da Malam Sabo, ya ce a duk lokacin da suka je gonakinsu, akan sace su a yi garkuwa da su don biyan kudin fansa ko kuma a koro su su dawo gida ba shiri. Ya bayyana sunayen wasu kauyuka, inda masu garkuwa da mutanen ke zama, wadanda suka hada da Gurguzu da Kwate da Maguzawa Mai Giginya da Kwaten Danmasani da kuma kauyen Faka.

Malam Sabo, ya yi kira tare da roko ga hukumomin tsaro su ziyarci wadannan kauyuka domin ceto al’ummar wauraren daga kangin ’yan bindigar masu garkuwa da mutane.

Wani manomin, mai suna Aliyu Ibrahim ya ce: “Na share makonni da yawa ban je gonata ba, saboda ina cikin matsanancin tsoro. Muna bukatar jami’an tsaro su kawo mana dauki, ana yi mana barazana da abincinmu kuma raykanmu na cikin hadari. Sana’armu ta noma a yankunanmu na Rigasa tana fuskantar barazana.”

Kakakin Hukumar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Yakubu Sabo Abubakar da Aminiya ta tuntube shi, ya musanta ikirarin mutanen na Igabi. “Wannan ba gaskiya ba e, domin kuwa har yanzu manoma a yankunan da suka ambata suna zuwa gonakinsu. Ayyukan masu garkuwa da mutane sun kau, domin kuwa ’yan sanda sun dauki matakin samar da tsaro a yankunan.

“Hukumar ’yan sanda a jihar ta dauki tsattsauran matakin tsaro domin magance duk wasu ayyukan ta’addanci da sauran laifuffuka a Kaduna. Kwanan nan dai matsalar da muke fuskanta, ita ce ta ’yan bindiga a yankin Birnin Gwari, duk da cewa mun kai jami’anmu da dama a yankin domin shawo kan duk wata barazanar tsaro a yankin,” inji shi.