✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu garkuwa da mutane sun yi ikirarin kashe Sumayya

Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da tagwayen nan na Zamfara da ’yar uwarsu Sumayya sun dauki alwashin kashe Sumayya idan ba a…

Masu garkuwa da mutane da suka yi garkuwa da tagwayen nan na Zamfara da ’yar uwarsu Sumayya sun dauki alwashin kashe Sumayya idan ba a biya su kudin fansarta ba.

Masu garkuwan suna neman makudan kudi ne da ya kai Naira miliyan 20 daga iyayen Sumayya, idan kuma ba a ba su ba, to nan zuwa gobe za su kashe ta.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa, domin su nuna da gaske suke yi, masu garkuwa da mutanen sun kashe Surajo Umar, wanda makwabci ne na su Sumayya wanda shi me yake hannunsu.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne aka yi garkuwa da tagwayen mata biyu Hassana da Hussaina da ita Sumayya da ke dauke da juna biyu.
Lamarin ya faru ne a lokacin da tagwayen suke shirin yin aure, sannan daga bisani aka karbo tagwayen aka baro Sumayya a wajen ’yan bindigan.