Mataimakin shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dokokin jihar Kaduna Shehu Yunusa Pambeguwa, ya bayyana yadda masu satar mutane suka aiko masa da wasikar barazana.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da Kwamishinan tsaro da Al’amuran cikin gida Samuel Aruwan, ya bayyana a gaban Majalisar domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa a ranar Litinin.
Dan Majalisar ya kara da cewa, babu isashshen tsaro a Majalisar haka kuma a gidajensu wanda hakan ke bai wa ‘yan bangar siyasa damar zuwa ofisoshinsu suna yi masu barazana.
“Babu tsaro a nan majalisa haka kuma a gidajen mu domin ni kaina nan sai da aka aiko min da wasika daga masu garkuwa da mutane da sauran su. Har takai na nemi a bani ’Yan Sanda domin kare gidana saboda anan iyalina suke,” in ji shi.