Masu ikirarin jihadi sun fi kashe Musulmi – Rahoton Ingila

Wani rahoton da Gidauniya Tony Blair da ke Ingila ta fitar ya ce kungiyoyoyin da ke da’awar jihadi sun fi kashe Musulmi fiye da mabiya wani addini a duniya.

Gidauniyar wadda ta ce ta yi bincike da sa-ido kan ayyukan ta’ddanci tun daga shekarar 2017 a duniya ta ce kashi 70 na wadanda aka kashe Musulmi ne wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Sai da ta ce a Musulmin ma ’yan Shi’a ne aka fi kashewa, kuma ba ya ga Musulmi, mabiya addinin Kirista ne aka fi kashewa.

Rahoton kuma ya sanya kasashen Afirka shida a jerin kasashe goma da suka fi fuskantar hare-hare mafiya muni na kungiyoyi masu da’awar jihadi.

Najeriya ce ta uku a jerin kasashen da aka fi kashe mutane a duniya bayan Syria da Somaliya. Sauran kasashen Afirka da suke fuskantar kashe-kashen sun hada da Mali da Kamaru da Nijar da Masar da Burkina Faso da Kenya.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya bayyana yawan kungiyoyi 97 masu da’awar jihadi da ke kai hare-hare a kasashe 46, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Kungiyar Boko Haram da ta addabi kasashen yankin Sahel, rahoton ya ce ta kai hare-hare a Najeriya sau 226, sannan ta kai hare-hare 187 a kasashen Kamaru sai Chadi sau 187, tare da sace mutum 370.

Rahoton ya ce duk da ana ikirarin murkushe kungiyoyi, kamar ISIS a Iraki da Syria da Boko Haram a Najeriya, hakan ba yana nuna an kawo karshensu.

A shekara biyu da suka gabata rahoton ya ce sama da mutum dubu 120 aka kashe a hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, kuma kasashe 68 al’amarin ya shafa da suka hada da manyan kasashen Turai wato Birtaniya da Faransa da kuma Jamus.

Barista Abdu Bulama Bukarti, mai nazari kan kungiyoyin ta’addanci a Afirka a gidauniyar ta Tony Blair ya shaida wa BBC cewa “girman matsalar ta fi yawa a kasashen Afirka.

“Ya kamata gwamnatocin kashsen Afirka su fahimci wannan matsalar da ta shafe su, sannan su hada kai domin kawo karshenta,” inji shi.

Rahoton ya ce ayyukan masu ikirarin jihadi na ci gaba da zama babbar barazana a duniya.

 

 

 

 

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya