✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kanjamau dubu 188 ba sa shan magana a Benuwai

Akalla masu kanjamau dubu 188 ne a Jihar Benuwai ba sa shan maganin cutar. Shugaban Gidauniyar AIDS Healthcare ta Jihar, Dokta Uduak Effiong ce ta…

Akalla masu kanjamau dubu 188 ne a Jihar Benuwai ba sa shan maganin cutar.

Shugaban Gidauniyar AIDS Healthcare ta Jihar, Dokta Uduak Effiong ce ta sanar da haka lokacin da take zantawa da manema labarai a Makurdi.

Dokta Effiong ta ce an samu kididdigar ce daga Hukumar NHAIIS, mai bayar da kididdiga kan cutar, inda ta ce wannan na nuna yawan masu dauke da kwayar cutar ba sa shan magani ne kawai.

Ta ce an samu raguwar masu dauke da cutar a Jihar Binuwei daga kashi 14.1 zuwa kashi 5.3, inda ta dawo ta biyu a bayan Jihar Akwa Ibom mai kashi 5.5.

Shugabar ta kara da cewa abin da suke so shi ne su dukufa wajen yaki da shi a yanzu shi ne yadda ake kara samun yawan masu cutar a tsakanin matasa ’yan shekara 20 zuwa 24, wadanda a cewarta suke yawan jima’i ba tare da kariya ba.

A jawabin, Manajan Kasuwanci na cibiyar, Stebe Aborisade ya ce a bikin ranar masu dauke da cutar kanjamau ta bana, za su koyar da akalla matasa 50 hanyoyin kariya da lura da cutar, domin su koma garuruwansu su isar da sako.