✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu kiran Buhari ya kori Abba Kyari ba ’yan Jam’iyyar APC ba ne – Mai Kassu

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ACPN ta Kasa, Shiyyar Arewa, Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo ya ce mutanen da suka yi zanga-zangar neman Shugaban Kasa Buhari ya…

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar ACPN ta Kasa, Shiyyar Arewa, Alhaji Ibrahim Mai Kassu Goronyo ya ce mutanen da suka yi zanga-zangar neman Shugaban Kasa Buhari ya tsige Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Abba Kyari ba ’ya’yan Jam’iyyar APC ba ne, kuma ba sa son samun nasara ga Shugaba Buhari a mulkinsa wa’adi na biyu.

Alhaji Ibrahim Kassu ya bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata a Sakkwato, inda ya ce duk da shi dan jam’iyyar adawa ce dole ne ya yi magana kan wannan lamari domin Shugaba Buhari Najeriya yake mulki, ba zance jam’iyya ko yanki ba. “Ba na sa ran wadannan mutane magoya bayan Jam’iyyar APC ce, ganin ba su da kishin kasar nan. Kowa ya san Buhari mai gaskiya ne da adalci, hakan ya sanya ya jawo aminansa kusa da shi don su taimake shi da shawarwarin da za a ci gaba kuma suna iyakar kokarinsu don ganin shugabancinsa ya zama abin alfahari ga mutanen kasa,” inji shi.

Ya ce zarge-zargen da suke yi bai  dauke su gaskiya ba, domin ba su Abba Kyari ne ke rike da jagoranci ba, iyakarsu bayar da shawara. Ya ce a saninsa  Buhari  ba ya tsoron kowa sai Allah, ya aminta da mutanen nan ne ya jawo su kusa da shi, don haka masu soke-soken ba su nufin alheri  ga kasar nan.

Ya ce “Alkawarin da Shugaba Buhari ya yi na ba za a samu tsaiko ba wurin gudanar abubuwan gwamnati ba, ya kamata mutane su sani duk abin da mutum zai yi sai ya bi a hankali, kowa ya san Buhari mutum ne adali don haka dole ne sai ya tsaya ya tantance wanda zai bai wa amana.”

Game da yadda yankinsa a Sakkwato ke fama da matsalar tsaro, ya ce gwamnatin jihar na kokari sosai, amma dai bai isa ba sai mutane sun taimaka mata a harkokin tsaron. Ya ce a cire yaudara da son musgunawa a dawo da zumunci a tsakanin juna, duk abin da wani ya gani da bai aminta ba ya sanar da hukuma a rika ba jami’an tsaro bayanai da kuma kalamai masu karfafawa.