✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Masu nuna wariyar launin fata kun ji kunya – Balotelli

Mario Balotelli ya buga kwallo cikin ’yan kallo sannan ya yi barazanar zai fice daga filin wasan bayan an yi masa kalaman wariyar launin fata…

Mario Balotelli ya buga kwallo cikin ’yan kallo sannan ya yi barazanar zai fice daga filin wasan bayan an yi masa kalaman wariyar launin fata a wasan da Berona ta doke kungiyarsa ta Brescia a gasar Serie A ta Italiya.

An dai tsayar da wasan cak lokacin da dan kasar Italiyan, mai shekara 29, ya rike kwallon da hannunsa a minti na 54. Abokan wasansa na Brescia da kuma mahukuntan wasan sun yi ta lallashinsa kan ya ci gaba da wasan.

Balotelli ya rubuta a shafinsa na Instagram: “Mutanen nan da suka kamanta ni da biri kun ji kunya! Kun ji kunya!!”

Sannan ya saka wani bidiyo na wasu magoya baya suna yi masa ihun wariyar launin fata tare da kwatanta shi da biri.

Ya kara da cewa: “A gaban yaranku da matanku da iyayenku da abokanku da shakikai….kun ji kunya!

“Na gode wa abokan wasana da irin goyon bayan da suka ba ni a ciki da wajen fili da kuma irin sakonnin da na samu daga gare ku. Na gode sosai. Kun tabbatar da cewa ku maza ne ba irin wadancan ba. #Notoracism.”

Bayan an lallashi Balotelli ya ci gaba da wasan, sai alkalin wasan Maurizio Mariani ya fara aiwatar da matakan yaki da wariya.

An yi sanarwar da ta yi gargadi ga magoya baya cewa idan suka ci gaba da wannan danyen aikin to za a dakatar da wasan baki daya.

Balotelli ya karasa wasan har ma ya ci kwallo daya a minti na 85, sai dai kungiyarsa ba ta iya farke ta biyun ba.

U-17:  An yi waje da Golden Eaglets

An yi waje rod da ayarin ’yan wasan Najeriya na Golden Eaglets da ci 3-i inda kungiyar ’yan wasan Netherlands ta yi waje da ita a wasan zagaye na biyu na gasar cin Kofn Duniya na ’yan kasa da shekara 17, a shekaranjiya Laraba.

Wasan da ke gudana a kasar Brazil Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ce take shiryawa.